logo

HAUSA

Daga Kin Gaskiya Sai Bata

2022-07-04 19:59:43 CMG Hausa

Yayin da yanayin tattalin arzikin kasashen duniya ke kara fuskantar halin rashin tabbas, kana kasashe da dama na cigaba da fafutukar yadda zasu cike komadar tattalin arzikin dake addabarsu, a hannu guda kuma, wasu daga cikin manyan kasashe masu karfin fada aji ta fuskar tattalin arzikin su ma suna dandana irin tasu kudar. Koda yake, wasu kasashen suna girbar abinda suka shuka ne a samakon daukar wasu matakai na bisa son zuciyarsu, ko kuma sun dauki matakan a bisa kuskure, ba tare da sun yi dogon tunani mai zurfi gabanin daukar irin wadannan matakai ko kuma yanke irin wannan danyen hukunci ba, wanda galibin wadannan matakai nadama ce ke biyo bayan yankesu, sannan lamarin yayi matukar haifar da mummunan tasiri tare da jefa alummunsu cikin halin ha’ula’i. Alal misali, a karshen wannan mako, wasu masanan kasar Amurka da dama suna ci gaba da yin kira ga gwamnatin shugaban kasar Amurka Joe Biden, da ta soke harajin da aka sanya a lokacin gwamnatin Trump kan kayayyakin da ake shigo da su daga kasar Sin, inda suka jaddada cewa, kawo karshen yakin ciniki a tsakanin kasashen Sin da Amurka zai yi matukar amfanawa Amurkawa. Anton Bekkerman, wani masanin tattalin arzki a fannin aikin gona ne, kana darakta cibiyar nazarin aikin noma ta jahar New Hampshire ya ce, “lokaci ya yi da ya kamata a fara tunanin yadda za a ci gaba, maimakon kirkiro wani abin da zai mayar da hannun agogo baya,” a cewar masanin, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban sashen nazarin kimiyyar rayuwa da aikin gona a jami’ar New Hampshire ta Amurka. Ya ce, kara kudaden harajin kwastan ba manufofi ne masu alfanu ba, kamar yadda ya bayyana a zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a baya-bayan nan. Shi ma Vincent Smith, masanin tattalin arziki, kuma shehun malamin jami’ar Montana, ya bayyana a kwanan nan cewa, “Za a iya bayyana takaddamar kasuwancin a matsayin wani babban koma bayan tattalin arziki da gwamnatin Trump ta aiwatar, saboda abin takaici ne da rashin tunani game da hakikanin yadda duniya ke gudana, wanda wasu daga cikin mashawartan tsohon shugaban suka dinga ingiza jagoran kasar na wancan lokaci.” Tun a farkon wannan shekara, wasu alkaluman da sashen ayyukan gona na Amurka ya fitar sun nuna cewa, yakin cinikin da gwamnatin Trump ta assasa, ya jawowa fannin aikin gonar Amurka hasarar dalar Amurka kusan biliyan 27 a cikin shekaru biyun da suka gabata. Ko shakka babu, wannan al’amarin ya haifar da mummunan tasiri ga tattalin arzikin Washingtom, kuma abu mafi muhimmanci shine, ya kamata gwamnatin Biden ta sake tunani, domin ance, “ita gaskiya bata bukatar ado,” kuma “daga kin gaskiya sai bata.” (Ahmad)