logo

HAUSA

Shugaban Ghana ya bukaci da a zage damtse wajen tunbuke tushen ta’addanci a yammacin Afirka

2022-07-04 10:03:35 CMG Hausa

Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya yi kira ga shugabannin kasashe mambobin kungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta yamma wato ECOWAS, da su zage damtse wajen aiwatar da matakan tunbuke tushen ayyukan ta’addanci daga shiyyar.

Akufo-Addo, wanda ke ban kwana da shugabancin kungiyar na karba karba, ya yi wannan kira ne a jiya Lahadi, cikin jawabinsa na kaddamar da taron shugabannin kungiyar karo na 61 a birnin Accra, fadar mulkin kasar ta Ghana.

Ya ce "Shiyyarmu na ci gaba da zama wuri da ’yan ta’adda ke hari ba ji ba gani, lamarin dake haifar da asarar rayukan mutane da ba su ji ba su gani ba, da sabbaba mummunan yanayin jin kai a kasashen da suke fuskantar wannan kalubale”.

Mr. Akufo-Addo ya kara da cewa, a yanzu haka ’yan ta’addan yammacin Afirka, na maida hankali ba kawai a yankin Sahel ba, har ma zuwa yankunan bakin teku dake makwaftaka da shiyyar.

Daga nan sai ya sake jaddada bukatar aiwatar da tsarin yankin, na yaki da wannan matsala, da tsara sauran matakai masu nasaba da hakan, don kawo karshen barazanar ta’addanci da rashin tsaro a yammacin Afirka.  (Saminu)