logo

HAUSA

Ye Shuhua: Ba da gudummawa ga ci gaban sha’anin sararin samaniya na Sin

2022-07-04 16:08:20 CMG Hausa

 

Kan Ye Shuhua ya kasance cikin taurari tun da ta san kanta. Tun tana karama, Ye take son kallon taurari a sararin samaniya. A lokacin, ba ta san kallon taurarin zai zama sana’arta ba, har ma ta zama fitacciyar mai ilimin taurari a duniya. Amma wannan shi ne labarin rayuwarta. Ta cimma nasarori da dama a rayuwarta, ita ce shugabar cibiyar sa ido kan nazarin taurari ta Shanghai ta SAO, wadda ke karkashin kwalejin kimiyya ta kasar Sin, daga shekarar 1981 zuwa 1993, kuma ita ce ta kirkiro amfani da lokaci na kasar Sin wato “Agogon Beijing”, a babban yankin kasar. Ye ta kasance mace daya tilo dake da kwarewar zama shugabar cibiyar SAO. Mutane da dama a kasar Sin, har ma da wasu sassan duniya, na ganin Ye a matsayin mai matukar son taurari. A hakika dai, da amincewar kungiyar inganta ayyukan nazarin taurari ta duniya, an sanyawa wata karamar duniya sunan Ye. A bayyane yake cewa, Ye ta yi kyakkyawan rayuwa, inda ta zama tauraruwa.

Cikin gomman shekarun da suka gabata, Ye ta shirya, ko kuma ta shiga an dama da ita, wajen gudanar da shirye-shiryen bincike. Ta kuma kirkiro wani reshe na kimiyya a kasar Sin wato Astro-geodynamics, mai nazarin motsin duniya. Karkashin shugabancinta, masana kimiyya na kasar Sin da dama sun samu muhimman sakamako a ayyukansu, inda suka samu yabo daga takwarorinsu na kasashen waje.

An haifi Ye Shuhua a birnin Guangzhou, hedkwatar lardin Guangdong na Sin a watan Yunin 1927. A lokacin da take da shekara 9, iyayenta suka koma Hong Kong. Kamar yadda Sinawa kan ce, “Tsirrai da dama na tsirowa a lambun da ba a shuka su ba.” A lokacin da take karama, tana kaunar adabi. Sai dai, iyayenta sun sa ta karanci fannin kimiyya, domin a ganinsu, za ta fi saurin samun aiki bayan ta kammala karatu. A 1945, ta samu gurbin karatu a sashen lissafi da ya shafi ilimin taurari, na jami’ar Sun Yat-Sen dake Guangzhou. Ita ce ta fi samun maki mai yawa a jarrabawar neman gurbin karatu a lokacin. Ye ta ce, “A lokacin da na shiga jami’a, na ji tamkar wata kofa ta bude a gabana. Na tsunduma cikin karatu, kuma sai na gano cewa, sararin samaniya na da matukar ban sha’awa fiye da tunanin mutum.”

Ye ta koma Hong Kong a shekarar 1949, bayan ta kammala jami’a. A shekarar 1951 kuma, aka dauki Cheng Jitai, mijinta, aiki a matsayin malamin lissafi a jami’ar Fudan dake birnin Shanghai, don haka, Ye da Cheng, suka koma Shanghai. Sai dai, Ye ta fuskanci matsala, inda ake ganin mata ba za su iya aikin binciken taurari ba. Ba ta karaya ba, ta rubuta wasika zuwa ga Zhang Yuzhe, shugaban cibiyar sa ido kan nazarin taurari ta Purple Mountain na wancan lokaci, wanda ke birnin Nanjing, hedkwatar lardin Jiangsu dake gabashin kasar Sin, inda ta zayyana dalilan da ya sa ya kamata ya dauke ta aiki. Ye ta burge shi, don haka ya bada shawarar a dauke ta aiki a cibiyar Xujiahui, wadda wani reshe ne na cibiyar Purple Mountain. Don haka, Ye ta zama mace ta farko mai bincike da aka dauka aiki a cibiyar.   

A farkon shekarun 1950, jim kadan bayan kafa Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin, kasar ta yi rashin kwararru a fannin ayyukan ilimin taurari. A lokacin da Ye ta fara aiki a cibiyar Xujiahui, masu bincike 4 ne kadai ke akwai, ciki har da ita. Aikin Ye shi ne, tabbatar da lokaci da nazarin taurari da auna sauyawar wurarensu. Ta ji dadin aikin, duk da maimaicinsa da nazarce-nazarce da tattara bayanai.

Bisa la’akari da rashin fasahohi da kayayyakin aiki na zamani a kasar, a shekarun 1950, kasar Sin ta kasance a bayan galibin kasashe wajen tantance ainihin lokaci. Ye Shuhua a matsayin jagora, ta yi aiki tukuru tare da abokan aikinta, wajen samar da tsarin lokaci na kasar Sin. Sun samu gagarumin sakamako a bincikensu, inda a shekarar 1965, kasar Sin ta fara amfani da agogon Beijing, wanda ake amfani da shi a babban yankin kasar. Kasar ta daina amfani da siginar lokaci ta wasu kasashe wajen tantance nata lokacin. Har ma ta yi tsalle zuwa kasa ta biyu, bayan Faransa, a fannin daidaitaccen lokaci. Fara amfani da lokacin na agogon Beijing, gagarumar nasara ce a tarihin kasar Sin, musammam la’akari da yadda ya ba da gudunmuwa ga bangaren tsaron kasar da ma ci gaban tattalin arzikinta.

 A 1973, Ye Shuhua ta gabatar da shawarar samar da fasahohin amfanin tsarin VLBI, domin samarwa masana ilimin taurari hotunan abubuwan dake sararin samaniya daga wuri mai nisa. Shugabannin cibiyar SAO sun amince da shawarar ta Ye Shuhua. Da shekara ta zagayo, hukumar kula da tekuna da yanayi ta Amurka ta gayyaci Ye ta kai ziyara na tsawon watanni 3, domin nazarin yadda ake amfani da tsarin VLBI.

A 1981, aka nada Ye a matsayin shugabar cibiyar SAO. Kuma a wannan shekara, cibiyar ta kaddamar da aikin samar da tsarin VLBI. A 1986 kuma, aka kammala tsara kudurin samar da tsarin VLBI na kasar Sin, wanda ya bayyana baki dayan tsarin nazarin taurari na kasar. A sannan kuma aka nada Ye matsayin babbar darakta mai kula da aikin.

Saboda namijin kokarinta wajen jagorantar ma’aikatan cibiyar domin inganta ayyukansu na bincike, masu ruwa da tsaki a fannin ilimin taurari na kasar Sin, suka kama kafar takwarorinsu na duniya a wannan fanni a shekarun 1980. A duk lokacin da abokan aikinta ko na hulda suka yabawa irin hangen nesanta, Ye ta kan ce “Damar na gabana. Yaya za a yi in gaza amfani da ita?”. A wajen Ye, bukatun kasa sun zarce komai. Wannan ne ya ba ta kwarin gwiwar samun gagarumar nasara a fannin kimiyya.

Yayin taro na 21 na kungiyar masana ilimin duniya da muhallin sararin samaniya da ya gudana a shekarar 1995 a Boulder na Amurka, Ye ta gabatar da wani shirin nazarin motsin duniya na yankin Asiya da tekun Fasifik ga mashirya taron domin neman sahalewarsu. “mun sha wahalar neman masu goyon bayan shirin, a karon farko a tarihi, masana ilimin taurari na kasar Sin, suka samu damar karbar bakuncin babban taron kasa da kasa,” cewar Ye.

An shafe shekaru da dama, amma Ye ta bar gagarumar tarihi. Ta cimma nasarori da dama a fannin bincike, tare da abokan aikinta, wadanda suka kai su ga samun kyaututtuka na kasa. A shekarar 1980, ta zama mambar kwalejin nazarin kimiyya ta kasar Sin. A 1985, ta zama mambar kungiyar masana ilimin taurari ta Birtaniya (RAS), daga 1988-1994 kuma, ta rike mukamin mataimakiyar shugaban kungiyar masana taurari ta duniya (IAU). A shekarar 1995, kungiyar mata ta kasar Sin ta sanya sunan Ye cikin fitattun matan kasar 10.  

Wasu daga cikin kawayenta, sun yi ta neman ta rika hutawa ta kula da kanta, ta yadda za ta ji dadin rayuwarta a gaba, maimakon haka, ta shiga aikin hidimtawa al’umma, musamam shirye-shiryen dake da nufin tabbatar da lafiyar mata da yara.

A matsayin masaniyar kimiyya, Ye na goyon bayan shirye-shirye kan ilimin kimiyya ga yara. Ta kan dauki lokaci domin koyawa daliban firamare da na makarantar midil, yadda za su gudanar da gwaje-gwaje. Haka kuma ta kan gabatar da lakca a rediyo da fina finai da talabijin domin kara wayar da kan mutane game da ilimin taurari.

Yayin wani babban taro na 4 game da mata a duniya da aka yi a Beijing a watan Satumban 1995, Ye ta gabatar da jawabi, inda ta karfafawa matan duniya gwiwar tsallake duk wani shinge, domin kokarin cimma burinsu da bayar da gudunmuwa.

Haka kuma yayin taron masana kimiyya na duniya da aka yi a Shanghai cikin watan Nuwamban 2021, ‘yan kallo da dama, sun yaba da jawabin da Ye ta gabatar cikin harshen turanci, inda ta karafafawa mata neman daidaito da takwarorinsu maza. Masu amfani da intanet da dama, sun ce sun amfana da jawabin, inda suka gane cewa, ya kamata mata su yi kokarin samun nasara a sana’o’insu ta yadda za a ji muryoyinsu a kasa, a bangarorin siyasa da tattalin arziki da zamantakewa. (Kande Gao)