logo

HAUSA

Ya kamata a yi taka tsan-tsan kan shan abubuwa masu gina jiki

2022-07-03 16:46:17 CMG Hausa

 

Wani sabon nazari da jami’ar Queensland ta kasar Australiya ta gudanar ya nuna mana cewa, abubuwa masu gini jiki da ke kunshe da bitamin daban daban ko kuma sinadaran ma’adinai suna kawo barazana kamar yadda magani ke yi, don haka ya kamata a yi taka tsan-tsan kan shan irin wadannan abubuwa masu gina jiki.

Masu nazari sun yi bayani da cewa, hakika dai abubuwa masu gina jiki da ke kunshe da bitamin, sinadaran ma’adinai, da sinadaran enzyme ko sinadaran Amino acids magunguna ne, wadanda wajibi ne hukumar sa ido kan magunguna ta kasa ta sa musu ido a tsanake. Amma wasu mutane sun mayar da irin wadannan abubuwa masu gina jiki a matsayin abubuwan da suke sha a kowace rana baya ga cin abinci yadda ya kamata.

Masu nazarin sun yi karin haske da cewa, kamar yadda magunguna suke yi, irin wadannan abubuwa masu gini jiki su ma suna kawo illa ga lafiyar mutane. Haka kuma masu harhada abubuwan gina jiki da ke kunshe da bitamin da sinadaran ma’adinai ba sa yi wa masu sayayya gargadi, dangane da illolin da kila abubuwan masu gini jiki za su haifar, ko illolin da za a samu sakamakon shan abubuwan masu gini jiki da sauran magunguna ko kuma illolin da za a samu idan aka sha abubuwan masu gini jiki da yawa fiye da yadda ake bukata. Don haka mutane masu yawa ba su san cewa, watakila shan wasu nau’ikan abubuwa msu gina jiki fiye da kima zai kawo musu hadari ba.

Masu nazarin sun kara da cewa, hakika dai sakamakon kasancewar irin wadannan barazana ga lafiyar mutane, ya sa aka ayyana wasu abubuwa masu gini jiki a matsayin magungunan da tilas ne likita su bayar. Har ila yau kuma watakila akwai bitamin ko sinadarin ma’adini iri daya a cikin wasu nau’ikan abubuwa masu gina jiki, shi ya sa idan ana shan irin wadannan abubuwa masu gina jiki, to, kila za a shigar da wani nau’in bitami ko sinadarin ma’adini da yawa fiye da yadda ake bukata a lokaci guda.

Ban da haka kuma, masu nazarin suna ganin cewa, yadda wasu mutane suka gaskata amfanin abubuwa masu gina jiki fiye da kima, zai sanya su kashe kudade da yawa, amma ba kiyaye lafiyarsu ba, har ma su kan bata lokaci da jinkirin ganin likita a lokacin da ya fi dacewa. Don haka madam Zhang Chuji, likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta ba da shawarar cewa, a lokacin da masu aikin jinya suka tambayi mutane tarihinsu na fama da ciwo, kamata ya yi su kimanta yadda suke shan abubuwa masu gina jiki, su kuma ba su shawarar kiwon lafiya, a kokarin hana su shan abubuwan masu gini jiki da yawa fiye da yadda suke bukata. (Tasallah Yuan)