logo

HAUSA

Shugaban Najeriya Ya Yi Maraba Da Isowar Jirgin Ruwan Farko A Tashar Jiragen Ruwa Da Ke Ruwa Mai Zurfi Ta Lekki

2022-07-03 16:30:50 CMG Hausa

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya yi maraba da samun nasarar isar jirgin ruwan farko zuwa tashar jiragen ruwa da ke ruwa mai zurfi ta Lekki, wacce ita ce tashar jiragen ruwa da ke ruwa mai zurfi ta farko a kasar da ake gudanar da aikin gina ta a Lagos, cibiyar kasuwancin kasar.

Babban jirgin ruwan dakon kaya mai samfurin ZHEN HUA 28, ya taso ne daga yankin Hong Kong na kasar Sin, ya kuma isa kasar Najeriya a ranar Juma’a, wanda ke dauke da manyan injuna guda 3 da ake amfani da su wajen loda kayayyaki daga jiragen ruwa zuwa gabar teku, da wasu manyan injuna guda 10 da ake amfani da su wajen sauke kwantainoni daga cikin manyan jiragen ruwan dakon kaya a gabar teku, kamar yadda shugaba Buhari ya bayyana ta bakin mai taimaka masa a fannin yada labarai Femi Adesina.

Shugaban Najeriyar ya taya murna ga dukkan masu ruwa da tsaki a fannin sufuri ta ruwan kasar, inda ya bayyana cewa, amincewa da ya yi na gina sabbin tashoshin jiragen ruwa guda hudu a kasar, ciki har da tashar jiragen ruwa da ke ruwa mai zurfi ta Lekki, zai taimaka matuka wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.
A cewar sanarwar, matakin zai kuma taimaka wajen samar da guraben ayyukan yi masu tarin yawa, da janyo jarin kasashen waje, da kuma kara azama kan yin kasuwanci cikin sauki a kasar.

Shugaba Buhari ya kara da cewa, amfanin teku da amfanin ruwa suna da matukar muhimmanci ga inganta zaman rayuwar al’ummar Najeriya, don haka a cewarsa, gwamnati za ta yi iyakar kokarinta wajen bunkasa fannin don kyautata makomar fannin.(Ahmad)