logo

HAUSA

Ana sa ran yankin Hong Kong zai samu wani sabon ci gaba a cikin shekaru biyar masu zuwa

2022-07-02 16:41:26 CMG Hausa

Tun a lokacin babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, shugaban kasar Xi Jinping ya nuna kulawa matuka game da wadata da zaman lafiyar yankin musamman na Hong Kong, da moriyar jama'ar wurin da walwalarsu, inda ya yi nuni da cewa, ci gaba shi ne ginshikin raya yankin Hong Kong da kuma magance matsaloli daban-daban.

Shin ta yaya yankin Hong Kong zai samu sabon ci gaba cikin shekaru 5 masu zuwa?

A wajen bikin cika shekaru 25 da dawowar Hong Kong kasar Sin, da kuma bikin rantsar da gwamnati ta shida ta yankin, wanda aka gudanar a jiya Jumma’a, shugaba Xi Jinping ya gabatar da wasu dabaru 4 da yake fatan za su samar da ci gaban HK.

Dabarun hudu sun hada da "Mayar da hankali kan kara matsayin shugabanci" da "Kara karfin inganta ci gaba" da "Warware matsalolin da jama'a ke fuskanta ", da kuma "Wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali tare".

Xi Jinping ya kuma bayyana fatan sabuwar gwamnatin yankin za ta aiwatar da manufar "kasa daya, mai tsarin mulki biyu" tare da gudanar da ayyuka masu amfani, da kuma mai da hankali kan warware batutuwan da suka fi damun mazauna Hong Kong.

Xi Jinping ya bayyana cike da kauna cewa: "A halin yanzu, abin da ya fi jan hankulan jama'ar Hong Kong shi ne, fatan samun rayuwa mafi kyau, da zama a cikin gida mai fadi, da samun karin damammakin raya sana'o'i, da samar da ilimi mai inganci ga yara, da kuma samun kulawa mai inganci idan an tsufa." Don haka, ya bukaci sabuwar gwamnatin yankin da ta dauki bukatar al’umma, musamman ma fararen hula, a matsayin babbar manufarta ta gudanar da mulki.

Bisa la’akari da yadda ake matukar bukatar tsaro don samun ci gaba, shugaba Xi Jinping ya ce, bayan fuskantar tashin hankali, kowa yana jin cewa, Hong Kong ba zai kasance cikin rudani ba, kuma ba za a iya jinkirta ci gaban yankin ba. Yana mai cewa, dole ne a kawar da duk wani katsalandan tare da mai da hankali kan ci gabansa." (Mai fassara: Bilkisu Xin)