logo

HAUSA

Ma’aikatan agaji sun damu da matsalar yunwa da ta addabi mutane 30,000 a Maiduguri

2022-07-02 17:42:52 CMG Hausa

Ofishin kula da agajin jin kai na MDD, ya ce ma’aikatansa na bayyana damuwa game da karuwar matsalar karancin abinci da rashin tsaro, a sansanin ‘yan gudun hijira mafi girma dake Maiduguri, babban birnin jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya.

Ofishin ya bayyana a jiya cewa, an damu game da yadda aka shafe makonni ba a samu tallafin abinci ba a sansanin Muna. Lamarin da ya shafi ‘yan gudun hijira 30,000 daga cikin 50,000.

Ya kara da cewa, akwai kuma damuwa game da batun samar da kariya a sansanin da rashin damarmakin gudanar da harkokin rayuwa, wadanda ke tilastawa mutane komawa wasu wurare mara tsaro, inda suke fuskantar hadarin hari ko sacewa daga bata gari.

A cewar ofishin, ana fuskantar lamarin ne biyo bayan tsananin tabarbarewar rashin abinci a fadin yankin arewa maso gabashin Nijeriya. Inda ya ce wasu mutane miliyan 4.1 na cikin hadarin rashin abinci a wannan yanayi da ba a kai ga girbi ba, inda aka yi hasashen mutane 600,000 za su shiga yanayin bukatar agajin gaggawa.

Har ila yau, ofishin ya ce duk da karancin kudi, ma’aikatan agaji sun taimakawa mutane miliyan 1.8 a rubu’in farko na bana. Kana kaso 23 kadai aka samu na dala biliyan 1.1 da ake bukata na aiwatar da shirin agajin jin kai na shekarar 2022.

Bugu da kari, ofishin ya ce gwamnati na shirin rufe dukannin sansanonin ‘yan gudun hijira dake Maiduguri, babban birnin jihar Borno cikin wasu makonni masu zuwa, cikinsu kuma har da na Muna. (Fa’iza Mustapha)