logo

HAUSA

Kamfanin CRCC na kasar Sin ya kammala aikin samar da ruwan sha a Angola

2022-07-02 18:05:17 CMG Hausa

An kammala aikin samar da ruwan sha na Cabinda na kasar Angola, wanda kamfanin gine-gine na kasar Sin (CRCC) ya aiwatar, inda aka fara amfani da shi a ranar 30 ga watan Yuni. An ba da rahoton cewa, an gudanar da aikin ne bisa ma’aunin gine-gine na kasar Sin, wanda zai samar da ruwa mai yawan kyubik mita 50,000 a ko wace rana, tare da amfanawa mazauna yankin 600,000.

Gwamnan lardin Cabinda, ya bayyana cewa, aikin zai iya samar da ruwan famfo na sa’o’i 24 a ko wace rana, wanda hakan zai kawar da matsalar karancin ruwa da mazauna yankin ke fuskanta, sannan kuma zai yi tasiri mai kyau ga bangarorin masana'antu, da ilimi, al'adu, sufuri ta tashar jiragen ruwa da dai sauransu.

Baya ga haka, ya godewa kamfanin na kasar Sin saboda muhimmiyar rawar da ya taka wajen gudanar da aikin. (Mai fassara: Bilkisu Xin)