logo

HAUSA

MDD ta damu game da karuwar fadan kabilanci a Sudan ta kudu

2022-07-01 12:21:15 CMG Hausa

Majalisar dinkin duniya MDD, ta bayyana damuwa game da barkewar fadan kabilanci a Sudan ta kudu, wanda ta bayyana da cewa yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da kuma jikkatar wasu.

Wakilin musamman na babban sakataren MDD Antonio Guterres a Sudan ta kudu, Nicholas Haysom, yayi Allah wadai da rikici na baya bayan nan da ya barke a gabashi da kuma tsakiyar jahohin Equatoria, da Unity, da Warrap, da kuma jahar Jongeli, har ma da yankin hukumar mulki ta Abyei, inda ya bayyana cewa rikici ne da ya barke a tsakanin kungiyoyin masu dauke da makamai na unguwanni.

Haysom, wanda kuma shine shugaban tawagar shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a Sudan ta kudu (UNMISS), yayi gargadi game da yiwuwar karin barkewar fadan kabilancin a sakamakon karancin abinci wanda matsalar sauyin yanayi ta haddasa.(Ahmad)