logo

HAUSA

Shugaban Kongo DRC ya bukaci a yi gangamin nuna adawa da ‘yan tawaye

2022-07-01 12:18:18 CMG Hausa

A jiya Alhamis shugaban jamhuriyar demokaradiyyar Kongo DRC, yayi kira da a gudanar da gangamin wayar da kan al’ummar kasar don nuna adawa da ayyukan kungiyar masu dauke da makamai ta March 23 Movement ko kuma (M23) a takaice.

Shugaba Felix Tshisekedi, yayi wannan tsokaci ne a jawabin da ya gabatarwa ‘yan kasar na bikin cika shekaru 62 da samun ‘yancin kasar wanda ya kasance a ranar 30 ga watan Yunin shekarar 1960.

Sake bullar mayakan M23 na baya bayan nan, ya haifar da tashin hankali da barkewar rikici a gabashin Kongo DRC, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar fararen hula da raunatar wasu da dama, gami da tilaswa wasu tserewa daga gidajensu.

A lokacin taron shugabanin kasashen kungiyar raya al’ummar gabashin Afrika EAC karo na uku, wanda aka gudanar a ranar 20 ga watan Yuni, shugabannin sun amince da tura karin dakarun tsaro na shiyya domin daidaita yanayi da kuma samar da cikakken tsaro da zaman lafiyar a Kongo DRC.(Ahmad)