logo

HAUSA

’Yan kasuwar Sin da Afrika sun daddale yarjeniyoyin kasuwanci

2022-07-01 18:14:53 CMG Hausa

’Yan kasuwa a kalla 73, kwastamomin bankin Stanbic na Botswana, daga bangarorin kasuwanci 9 ne suka baje hajojinsu ga sama da Sinawa 200 masu shigo da kayayyaki kasar, wadanda suka taru a Changsha, babban birnin lardin Hunan, inda daga bisani bangarorin biyu suka daddale yarjeniyoyin kasuwanci. 

Bankin Stanbic da abokin huldarsa bankin ICBC na kasar Sin, da hadin gwiwar dandalin baje kolin cinikayya da tattalin arziki tsakanin Afrika da Sin ne suka dauki nauyin taron hada ’yan kasuwar, wanda ya gudana a ranar Laraba ta kafar bidiyo. Taron ya gudana ne a Gaborone, babban birnin kasar Botswana.

Shugaban sashen kula da harkokin tsakanin Sin da Afrika a bankin Stanbic na Botswana, Philip Myburg, ya ce bankin Stanbic da bankin ICBC sun ya shafe sama da shekaru 10 suna hadin gwiwa da zummar saukaka harkokin cinikayya tsakanin Sin da Afrika. (Fa’iza Mustapha)