logo

HAUSA

Jakadan Sin ya bukaci a dauki matakan bai daya don magance rikicin gabashin Kongo DRC

2022-06-30 10:47:28 CMG Hausa

Jiya Laraba wakilin kasar Sin ya bayyana halin da ake ciki a shiyyar gabashin jamhuriyar demokaradiyyar Kongo DRC da cewa abin damuwa ne matuka, sannan yayi kira ga dukkan bangarorin da lamarin ya shafa da su hada kai domin daukar matakai na bai daya don magance tashe-tashen hankula a shiyyar.

Dai Bing, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, ya bayyanawa taron kwamitin sulhu na MDD kan batun rikicin DRC cewa, a matsayinta da muhimmiyar abokiyar hulda ga shiyyar, kasar Sin tana fatan dukkan bangarorin za su kiyaye moriyar juna, da martaba al’amurran dake shafar juna, kana su bi kyakkyawar hanya mafi dacewa wajen warware rashin fahimtar juna a tsakaninsu ta hanyar tattaunawar sulhu, da tuntubar juna, da nufin magance tashe-tashen hankula a shiyyar.

A baya bayan nan dai sake bayyanar mayakan ’yan tawayen kungiyar (M23), ya yi matukar haifar da tashe-tashen hankula da rikici a gabashin Kongo DRC, lamarin da ya yi sanadiyyar kashewa da jikkata fararen hula da kuma tilastawa wasu tserewa daga gidajensu.

Dai Bing ya ce, wannan babban abin damuwa ne. Domin kawar da barazanar da ake fuskanta daga mayakan kungiyoyin masu dauke da makamai a gabashin DRC, tilas ne a dauki matakai na bai daya daga dukkan fannoni, in ji wakilin na Sin. (Ahmad)