logo

HAUSA

Ministar wajen Ghana ta bukaci a gaggauta daukar matakan dakile matsalar tsaro a shiyyar yammacin Afrika

2022-06-30 12:40:55 CMG Hausa

Shirley Ayorkor Botchwey, ministar harkokin wajen kasar Ghana, ta ce akwai bukatar daukar matakan gaggawa domin dakile matsalar tabarbarewar tsaro a yammacin Afrika.

Botchwey, wanda kuma ita ce shugabar taron majalisar ministocin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS), ta yi wannan kiran ne a wajen bude taron tattaunawa na majalisar shiga tsakani da wanzar da tsaro ta kungiyar ECOWAS karo 48.

Ta ce, duk da namjin kokarin da shugabancin kungiyar na shiyyar ke yi ba tare da nuna gajiyawa ba, amma har yanzu ana samun karuwar rikice-rikice da kaddamar da hare-hare a shiyyar.

Madam Botchwey ta jaddada cewa, hanya mafi dacewa ta samu tabbaci da ingantacciyar rayuwa ga al’ummar kasashen mambobin ECOWAS shi ne, a yi kokarin farfado da yanayin zaman lafiya da tsaron shiyyar. (Ahmad)