logo

HAUSA

Shugaban kasar Afrika ta tsakiya ya baiwa runkunin jiyya da Sin ta turawa kasar lambar yabo

2022-06-30 14:01:28 CMG HAUSA

Jiya Laraba, shugaban kasar Afrika ta tsakiya Faustin-Archange Touadéra, ya baiwa tawaga ta 18 ta runkunin jiyya da Sin ta tura kasar lambar yabo a fadarsa, inda likitoci 9 suka samu lambar yabo ta jami’an soja, masu aiki fassara da dafa abinci, suka samu lambar yabo ta barada

A yayin bikin, Faustin-Archange Touadéra ya nuna cewa, ya karrama runkunin da wannan lambar ne, don jinjinawa taimakon da suka bayar da ayyuka masu inganci da suka gudanar, da kuma bayyana matukar godiyar jama’arsa ga runkunin. Ya ce, a cikin shekara daya da ta gabata, tawagar ta baiwa iyalan jama’ar wurin makoma da farin ciki bisa ayyukan da suka yi, da inganta hadin gwiwar kiwon lafiya tsakanin Sin da Afirka da zurfafa dadadden zumuncin dake tsakanin jama’ar kasashen biyu.

Shugaban tawagar Chen yong ya ce, ya zuwa karshen watan Mayu, tawagar ta yi jiyyar mutane 20874, da yin tiyata 383.(Amina Xu)