logo

HAUSA

Kasar Sin Za Ta Mika Wa Zimbabwe Sabon Ginin Majalisar Dokokin Kasar Da Aka Kammala

2022-06-30 11:11:33 CMG Hausa

Yanzu haka, an kammala sabon ginin majalisar dokokin kasar Zimbabwe, wanda kasar Sin ta samar kudade da ma aikin gina shi, a matsayin kyauta ga kasar dake kudancin Afirka, kuma take shirin mika mata don fara aiki da shi.

An dai kwashe watanni 42 ne wajen kammala aikin, maimakon ainihin watanni 32 da aka tsara tun farko, saboda tsaikon da annobar cutar COVID-19 ta haifar. An dai fara aikin ginin ne a watan Nuwamban shekarar 2018.

Ginin wanda ke tsaunin Hampden mai tarihi, dake da tazarar kilomita 18 daga arewa maso yammacin Harare, babban birnin kasar Zimbabwe, yana da hawa shida ne, kana ya kunshi gine-ginen masu nasaba da sigogin kasashen Zimbabwe da na Sin.

A jiya ne, kamfanin gine-gine na Shanghai (SCG), dake kula da wannan aiki, ya kewaya da kafofin yada labarai, don duba ginin, gabanin mika shi a hukumance ga gwamnatin Zimbabwe nan gaba kadan.

Manajan ayyuka na kamfanin SCG Cai Libo ya ce, kammala aikin wani babban ci gaba ne ga abokantakar dake tsakanin kasashen Sin da Zimbabwe da ke ci gaba da bunkasa.(Ibrahim)