logo

HAUSA

An kara nuna shaidu kan makircin NATO na lalata duniya

2022-06-30 21:48:18 CMG Hausa

Wani sabon daftarin dabarun da aka zartas, a taron kolin kungiyar tsaro ta NATO da aka shirya a ranar 29 ga wata a birnin Madrid, ya ambato kasar Sin a karon farko, inda aka yi wa kasar Sin kazafi a matsayin "kalubale kan yankin Turai da na Atlantika".

Wannan wata babbar shaida ce da ke nuna cewa, NATO tana jujjuya baki da fari don kirkirar abokan gaba, hakan ya tabbatar da cewa, kungiyar NATO da ta ragu bayan yakin cacar baka, kalubale ne ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.

"NATO kawai kariya ce ta Amurka." Jaridar Le Soir ta kasar Belgium ta yi nuni da hakan. Idan aka waiwayi yunkurin kafuwar kungiyar NATO da kuma yadda aka fadada kungiyar, ba abu ne masu wahala a ga cewa, kungiyar wani makami ne da Amurka ke amfani da shi wajen kafa kungiyoyi da kuma yin arangama ba. 

Idan aka kara yin la'akari, kungiyar NATO ta sake taka rawa wajen damfarar siyasa, bayan da Amurka ta sanya kasar Sin a matsayin "babbar ‘yar takarar ta". Kwanan baya, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya yi ikirarin a cikin jawabinsa kan manufofin kasar game da Sin cewa, "za a tsara" muhalli bisa manyan tsare-tsare a kewayen kasar Sin. Taron kolin NATO na bana, ya gayyaci shugabannin Japan, Koriya ta Kudu, Australia da New Zealand a karon farko, da nufin kafa wata kungiyar NATO mai "Sigar Asiya-Pacific", da kuma "tsara" wani muhalli bisa manyan tsare-tsare a kewayen kasar Sin, wanda ya kasance wani yunkuri ne mai hadari, na gabatar da wani mummunan aiki na kirkirar abokan gaba a yankin Asiya-Pacific.

Kasar Sin ba ta taba tsoma baki cikin harkokin cikin gidan wasu kasashe ba, kana ba ta fitar da akidu zuwa kasashen waje, kuma ba ta shiga cikin ikon mallaka na sauran kasashe, ko tilastawa saura a fannin tattalin arziki, ko saka takunkumi ta bangare daya, ta yaya za ta iya kawo "kalubale" ga NATO? Sabanin haka, kungiyar NATO ta yi ikirarin cewa, ita "kungiyar tsaro" ce, amma a zahiri ta karya alkawarinta na kara fadada zuwa gabas, tana kuma tsallake kwamitin sulhun MDD akai-akai, don kaddamar da yaki da kasashe masu mulkin kai, inda ta zama wata ainihin “kungiyar mahara". (Mai fassara: Bilkisu Xin)