logo

HAUSA

Kasar Sin na kara azamar aiwatar da ajandar ci gaba mai dorewa ta MDD

2022-06-29 09:11:13 CMG Hausa

Yayin da ya rage shekaru 8 a kai ga wa’adin aiwatar da ajandar ci gaba mai dorewa ta MDD mai kunshe da burika 17, kasar Sin na ci gaba da kara azamar aiwatar da wadannan burika a cikin gida, ta yadda gudummawarta za ta ingiza nasarar da ake fatan cimmawa a duniya baki daya.

Fatan dai shi ne nan da shekarar 2030, duniya za ta samu gagarumin ci gaba a fannin yaki da fatara, da ingantuwar rayuwar al’umma, da kare muhalli.

Tuni kasar Sin ta yi nisa wajen cimma nasarori a fannonin nan 17, na wanzar da ci gaba mai dorewa, wadanda suka hada da yaki da talauci, da bunkasa samar da ilimi, da daidaiton jinsi, da samar da tsaftacaccen ruwa da makamashi, da guraben ayyukan yi da ci gaba. Kaza lika burikan sun hada da rage gibin ci gaba, da samar da birane masu inganci masu dorewa, da amfani da albarkatu yadda ya dace, da kare duniyar bil adama. Sauran su ne kare albarkatun ruwa, da na kasa, da wanzar da zaman lafiya da adalci tsakanin al’ummar duniya. Da kuma yin hadin gwiwa tsakanin dukkanin sassa domin cimma wadannan nasarori.

Idan mun kalli daukacin wadannan kudurori, za mu ga cewa, tuni kasar Sin ta yi nisa a fannonin yaki da talauci, wanda masana ke cewa nasarar ta Sin, ta zamo wani abu na bazata da aka jima ba a ga irin sa ba a tarihin duniya. Sauran sassan da Sin din ta yi zarra cikin jerin wadannan kudurori, sun hada da fannin kare muhallin bil adama, da muhallin halittu, da kyautata samarwa da amfani da makamashi, da kuma fannin fadada hadin gwiwar ta da sauran sassa, domin samar da ci gaba mai dorewa ga daukacin bil adama. (Saminu Hassan, Ibrahim Yaya, Sanusi Chen)