logo

HAUSA

An kaddamar da aikin gyaran filayen wasanni 4 a Senegal wadanda Sin ta dauki nauyi

2022-06-29 11:24:51 CMG Hausa

Ministan wasanni na kasar Senegal, Matar Ba, da jakadan kasar Sin a Senegal, Xiao Han, a ranar Talata sun jagoranci kaddamar da aikin gyara filayen wasanni hudu a Dakar, babban birnin kasar Senegal, wadanda kasar Sin ta samar da kudaden aikin.

Matar Ba, ya bayyana cewa, ayyukan gyaran filayen wasannin hudu, wani muhimmin al’amari ne, kuma gagarumin ci gaba, wanda ke kara bayyana zurfi da kuma ingantacciyar alaka da kyakkyawar abokantaka ta ’yan uwa dake tsakanin kasashen Senegal da Sin.

Ministan ya godewa muhimman taimakon da Sin ke bayarwa ga ci gaban  Senegal a fannoni da dama.

Jakadan Xiao Han ya ce, kasar Sin a ko da yaushe tana dora muhimmanci kan hadin gwiwa da Senegal a fannin wasanni, kuma muhimman sakamakon da ake samu karkashin hadin gwiwar bangarorin biyu, zai amfanar da zuriya masu zuwa nan gaba a kasar Senegal. (Ahmad)