logo

HAUSA

Masu muguwar niyya ba za su samu biyan bukata ba

2022-06-29 19:23:30 CMG Hausa

Ranar 1 ga watan Yuli mai kamawa rana ce ta cika shekaru 25 da yankin Hong Kong na kasar Sin ya koma gida. Da ma a karni na 19, kasar Birtaniya ta kwaci yankin daga kasar Sin, har ma ta yi shekaru fiye da 100 tana mulkin mallaka a can, kafin daga bisani sabuwar kasar Sin ta sanya Birtaniya mayar da yankin, a shekarar 1997, ta hanyar dokoki da shawarwari.

Amma kun san halayyar ‘yan mulkin mallaka. Kafin su bar wani wuri, to, dole ne su ta da rikici can, ta yadda za su ci gaba da yin tasiri a wurin nan gaba. Wannan batu dalili ne da ya sa ake samun rikicin kabilu a Najeriya, da kiyayar da ake samu tsakanin India da Pakistan, da dai sauran rikice-rikice daban daban, ciki har da wasu matsalolin da suka shafi yankin Hong Kong na kasar Sin.

Cikin shekaru fiye da 100 da Birtaniya take mulkin mallaka a Hong Kong, ba ta taba ba mutanen wurin hakkin dimokuradiya ba. Duk da haka, a shekarun 1990, wato dab da lokacin dawowar yankin Hong Kong karkashin mulkin kasar Sin, Birtaniya ta fara aiwatar da tsarin dimokuradiyya a Hong Kong, don neman samun rarrabuwar kawuna a fannin siyasa tsakanin al’ummun wurin, da kawo cikas ga mulkin da gwamnatin kasar Sin za ta gudanar a yankin Hong Kong. Sa’an nan Birtaniya ta taimaki mutanen yankin Hong Kong masu kishinta wajen zama manyan jami’ai da masu fada a ji, musamman ma a bangaren aikin ilimi da al’adu.

Ban da haka, Birtaniya ta yi hadin gwiwa da Amurka a kokarin sauya tunanin mutanen yankin Hong Kong. Misali, cikin littafin da kasar Birtaniya ta gabatar dangane da tarihin yankin Hong Kong, an bayyana isowar ‘yan Birtaniya a yankin a shekarar 1841 a matsayin mafarin tarihin yankin Hong Kong, ba tare da lura da alakar dake tsakanin yankin da kasa mahaifa ta Sin, wadda ke da tarihi na shekaru 5000 ba. Kana a nata bangare, kasar Amurka ta tallafi wasu hukumomi, ta “Asusun raya dimokuradiyya NED”, wadanda suka tsara littattafan karatun da aka yi amfani da su cikin jami’o’i 8 dake Hong Kong. Ta wannan hanya an dasa tunani na “kin jinin gwamnatin Sin” da “balle yankin Hong Kong” cikin kwakwalwar daliban jami’a.

Makarkashiyar siyasa da Amurka da Birtaniya suka kulla ta haifar da mummunan sakamako a shekarar 2019, inda aka samu zanga-zanga da bore a yankin Hong Kong, yanayin da ya dade har tsawon rabin shekara kafin a shawo kansa, wanda ya yi barna sosai ga al’ummar Hong Kong. Duk da haka, shugabannin kasashen Amurka da Birtaniya sun mara wa ‘yan bore baya, kana dimbin hukumomin kasar Amurka sun samar musu da tallafi, gami da ba su horo cikin wani dogon lokaci.

Ko da yake kasashen Birtaniya da Amurka sun yi kokarin ta da zaune-tsaye a yankin Hong Kong, amma kura ta lafa a yankin tun tuni, inda aka dawo da kwanciyar hankali. Dalilin da ya sa haka, shi ne domin gwamnatin kasar Sin ta dauki kwararran matakai na daidaita yanayin Hong Kong, inda ta gabatar da dokar tsaron kasa a Hong Hong, da daidaita tsarin zabe na yankin, don tabbatar da ganin cewa za a ba mutane masu kishin kasa damar gudanar da mulki. Ban da haka, an dauki matakai na karfafa tunanin al’umma na kasancewarsu ‘yan kasa. Sa’an nan wani dalili na daban da ya sa ake iya kwantar da kurar da ta tashi a Hong Kong, shi ne domin misalan wasu kasashen da aka gudanar da bore na neman juyin juya hali, irinsu Syria, da Libya, da Ukraine, sun sa al’umma fahimtar cewa ana neman ta da zaune tsaye don neman raunana yankin Hong Kong da kasar Sin baki daya kawai, maimakon kare hakkin jama’ar Hong Kong.

A nan za mu iya ganin cewa, ko da yake su kasashen Amurka da Birtaniya sun dade suna kokarin ta da rikici a yankin Hong Kong, amma a karshe dai, sun kasa samun biyan bukata, hakan ma ya nuna karfin al’ummar kasar Sin wajen kare kasarsu. Duk wata makarkashiyar da aka kulla ta neman raunana kasar Sin ba za ta samu nasara ba. (Bello Wang)