logo

HAUSA

Labaran wasan motsa jiki a wannan mako

2022-06-28 15:56:04 CRI

Sadio Mane Ya Koma Bayern Munich

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta tabbatar da cewa dan wasa Sadio Mane ya kammala komawa Bayern Munich kan kudi fam miliyan 35 kan yarjejeniyar kakar wasa uku.

A cikin yarjejeniyar, Liverpool za’a bawa Liverpool zunzurun kudi fam miliyan 27.4 da karin fam miliyan shida kan yawan buga wasa da wasu fam miliyan uku kan kokarin dan wasan da nasarorin da Bayern Munich za ta yi.

Mane, Mai shekara 30 a duniya Kuma dan kasar Senegal ya koma Liverpool ne akan kudi fam miliyan 34 daga Southampton a shekarar ta 2016.

Ya buga wasanni 269 a Liverpool inda ya zura kwallaye 120 sannan ya taimaka aka zura guda 48.

A shekaru shida da yayi a Liverpool, ya lashe gasar firimiyar Ingila da kofin zakarun turai na Champions league da FIFA Club World Cup da Eufa Super Cup da kofin kalubale na FA da kuma gasar Carabao Cup.

A farkon wannan shekarar ne dai ya taimaka wa kasar sa ta Senegal ta lashe kofin Nahiyar Afirka da kasar Kamaru ta karbi bakunci.

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta kammala Sayan dan wasan tsakiya na kungiyar FC Porto, Fabio Vieira, akan kudi fam miliyan 34.

Tun a satin daya gabata ne dai kungiyoyin biyu suka cimma matsaya bayan doguwar tattauna wa a tsakanin su

Vieira yana daya daga cikin ‘yan wasan da kociyan kungiyar, Mikel Arteta ya bukaci kungiyar ta siyo masa domin bunkasa tawagar a kakar wasa mai zuwa.

Bayan kammala Sayan Vieira, yanzu hankalin Arsenal zai karkata ga neman dan wasan Manchester City, Gabriel Jesus, wanda ake saran nan gaba kadan za’a shiga tattauna wa tsakanin kungiyoyin biyu.

 

 

Lukaku Ya Kusa Komawa Inter Milan A Matsayin Aro

Kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan tana ci gaba da tattaunawa da Rumelu Lukaku domin daukar dan wasan a matsayin aro na shekara daya kamar yadda babban jami’in kungiyar, Giuseppe Marotta ya sanar.

Dan wasa Lukaku dan tawagar Belgium mai shekara 29, ya ci kwallo 15 a dukkan wasannin da ya yi wa Chelsea a kakar da aka kammala har da takwas a karawa 26 a Premier League bayan ya koma kungiyar kan fam miliyan 97.5.

Lukaku, wanda ya bar Chelsea zuwa Everton kan kudi fam miliyan 28 a shekarar 2014, ya sake komawa Chelsea daga Inter a matakin wanda ta saya mafi tsada cikin watan Agustan shekara ta 2021 kan kwantiragin kaka biyar.

A kakar wasan data gabata ne dai Lukaku ya bayyanawa manema labarai a kasar Ingila cewa yana kewar kungiyar Inter Milan kuma yana fatan watarana zai sake komawa domin ya ci gaba da buga mata wasa.

Haka kuma jami’in ya sanar cewar suna kan batun daukar tsohon dan wasan Juventus Paulo Dybala da dan wasan Roma, Henrikh Mkhitaryan da mai tsaron ragar tawagar Kamaru, Andre Onana daga Ajax.

 

 

Kotu Ta Yankewa Eto’o Hukuncin Watanni 22 Saboda Kin Biyan Haraji

Wata kotu dake Ciudad de la Justicia da ke birnin Barcelona a kasar Spaniya ta yankewa tsohon dan wasan Barcelona da tawagar kasar Kamaru, Samuel Eto’o hukuncin watanni 22 na jeka gyara halinka bayan ya amsa laifin cogen harajin fam miliyan 3.2 a lokacin da yake buga wasa a Barcelona.

Har ila yau, alkalin kotun yace Eto’o zai biya kudin da ake binsa, da kuma tarar fam miliyan 1.55.

Manchester United Za Ta Mika Sabon Tayin Kudi Domin Sayan De Jong

Chelsea Tana Tattaunawa da Manchester City Kan Sayalen Sterling

Tun da farko dai masu shigar da kara a kasar ta Sipaniya sun zargi tsohon dan wasan na Inter Milan da Chelsea, Eto’o da kin bayyana kudaden shiga da aka yi tsakanin shekara ta 2006 zuwa 2009.

Tsohon dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo shima an taba gurfanar dashi a gaban kotu saboda yin cogen biyan haraji sannan Lionel Messi da Jose Mourinho da kuma Neymar suma an taba kaisu kotu da irin laifin.

Manchester United Za Ta Mika Sabon Tayin Kudi Domin Sayan De Jong

Wasu rahotanni daga Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United za ta kai sabon tayin kudi fam miliyan 70 domin sayan dan wasan Barcelona, Frankie De Jong.

Manchester United dai ta dade tana zawarcin matashin dan wasan mai shekara 25 kuma tuni ya amince da komawa kungiyar duk da cewa ba zata buga wasannin cin kofin zakarun turai ban a Champions League na bana.

Sabon kocin Manchester United, Erik ten Hag, ne yake fatan sake haduwa da dan wasan, wanda ya taba koyarwa a lokacin da suka yi aiki a Ajax ta kasar Holland.

 

 

Nketiah Ya Sake Sabunta Kwantiraginsa A Arsenal

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta tabbatar da cewa dan wasanta, Eddie Nketiah, ya saka hannu kan sabuwar yarjejeniyar kakar wasa biyar, domin ci gaba da buga mata wasa.

Daman dai kwantiragin dan wasan zai kare ne karshen watan nan, wanda ya buga wasanni 92 da cin kwallo 23, tun bayan da ya fara buga wasa a kungiyar a shekarar 2017.

Ya taka rawar gani daga karshen kakar da aka kammala a Arsenal, wanda ya buga wasa takwas da saka kwallo biyar.

 

 

Nketiah dai zai dinga saka riga mai lamba 14, bayan da ya yi amfani da mai lamba 30 a baya kuma ya fara da cin kungiyar Norwich City kwallo biyu a Caraboa Cup a wasansa na farko a 2017, yana cikin jerin ‘yan wasan Arsenal da suka lashe FA Cup da Community Shield a 2020.

Dan wasan shi ne kan gaba a tawagar matasan Ingila ‘yan kasa da shekara 21, mai kwallo 16 a raga a fafatawa 17 da ya yi mata sannan shi ne kyaftin a tawagar Ingila ta matasa ‘yan kasa da shekara 21 da ta lashe kofin Nahiyar Turai na matasa a 2021.