logo

HAUSA

Sudan ta kaddamar da hanyar jigilar kayayyaki ta ruwa kai tsaye zuwa kasar Sin

2022-06-28 10:03:21 CMG Hausa

A yammacin ranar Lahadi ne, kasar Sudan ta gudanar da bikin kaddamar da tashar jiragen ruwa mai suna, Sudan-China Express, dake zama layin farko na jigilar kayayyaki kai tsaye ta ruwa tsakanin kasashen biyu, a Khartoum,babban birnin kasar.

Ministan sufuri na kasar Sudan Hisham Ali Ahmed Abuzaid da jakadan kasar Sin a Sudan Ma Xinmin, na daga cikin jami'ai da wakilan 'yan kasuwa na kasashen biyu da suka halarci bikin.

Ma ya lura da cewa, kasar Sudan tana arewa maso gabashin Afirka, tana kuma kusa da yammacin gabar tekun Bahar Maliya, don haka, kasar tana da fa'ida ta musamman a fannin kasa, kuma ta kasance wata muhimmiyar hanya ta isar da kayayyakin kasar Sin zuwa Afirka tun zamanin da.

Xu Qun, shugaban kamfanin jigilar kayayyakin kasa da kasa mai suna Shanghai Greenroad International Logistics, kuma ma’aikacin jirgin ruwan, ya bayyana cewa, a ranar 11 ga watan Yuni, jirgin ruwan dakon kaya da ya kai nauyin tan 32,000, ya bar sabuwar hanyar da ta taso daga tashar jiragen ruwa ta Sudan, ana kuma sa ran zai isa wurin da ya nufa, wato tashar jiragen ruwa ta Qiandao dake gabashin kasar Sin a ranar 11 ga watan Yuli.(Ibrahim)