logo

HAUSA

Sin ta mika karin alluran riga-kafin COVID-19 miliyan 10 ga Habasha

2022-06-28 13:57:56 CMG HAUSA

 

A ranar Litinin gwamnatin kasar Sin ta mika karin alluran riga-kafin COVID-19 miliyan 10 na kamfanin hada magunguna na kasar Sin Sinopharm ga kasar Habasha.

Adadin na baya bayan nan, wanda ya kunshi alluran COVID-19 miliyan 10, ana fatan za su kara inganta shirin kasar Habasha na yin riga-kafin annobar COVID-19, kana za su taka muhimmiyar rawa wajen kawar da mummunan tasirin annobar ga tattalin arziki da zamantakewa.

Bikin mika riga-kafin ya samu halartar manyan jami’an gwamnatin kasar Habasha da jami’an diflomasiyyar kasar Sin a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha. (Ahmad Fagam)