logo

HAUSA

Sudan ta gurfanar da Habasha a gaban MDD game da kisan ’yan kasarta

2022-06-28 14:04:32 CMG HAUSA

 

A ranar Litinin kasar Sudan ta yanke shawarar shigar da korafi ga kwamitin sulhun MDD (UNSC), sakamakon kashe sojojin Sudan bakwai da kuma wani farar hula guda, bayan da aka yi garkuwa da su.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta kuma bukaci jakadanta dake kasar Habasha ya gaggauta komawa gida domin wata tattaunawa, sannan ta gayyaci jakadan Habasha a Khartoum tare da bayyana masa yadda Sudan ta yi Allah wadai da wannan al’amari.

A wata sanarwa, ma’aikatar ta yi Allah wadai da kakkausar murya game da mummunan laifin da sojojin Habashan suka aikata, wanda ya saba da dukkan dokokin kasa da kasa, inda aka kashe sojoji Sudan bakwai tare da farar hula guda bayan an yi garkuwa da su a wani yankin dake karkashin ikon kasar Sudan.

Sai dai ma’aikatar harkokin wajen Habasha ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twita cewa, al’amarin ya faru ne a wani yankin dake kan iyakar Habasha da Sudan a ranar 22 ga watan Yuni. Ta kara da cewa, lamarin ya faru ne a sakamakon musayar wuta tsakanin dakarun sojojin kasar Sudan da mayakan ’yan tawayen kasar. (Ahmad)