logo

HAUSA

Kalubalantar shawararar ziri daya da hanya daya? 'Yan siyasar Amurka suna son tashi hannu rabbana

2022-06-28 09:42:57 CMG Hausa

Amurka, wadda ba ta wadatu da ababen more rayuwa a cikin gidan ta ba , wai ita ce a zahiri za ta jagoranci aiwatar da abin da ake kira ayyukan samar da ababen more rayuwa a duniya. Wannan abin mamaki na rashin Imani,ya faru ne a taron G7 dake gudana a kasar Jamus.

A ranar 26 ga wata agogon wurin,a yayin taron, shugaban kasar Amurka Biden ya sanar da wani shiri na "hadin gwiwar samar da abubuwan more rayuwa na kasa da kasa " (PGII) inda ya yi ikirarin yin aiki tare da kasashen G7, don tattara dalar Amurka biliyan 600, don zubawa a jarin samar da ababen more rayuwa a duniya nan da shekarar 2027.

A yayin taron G7 da aka gudanar shekara guda da suka gabata, an gabatar da shawarar hadin gwiwa da ake kira "Sake gina duniya mai Kyau" (B3W), tare da shirin zuba jarin sama da dalar Amurka tiriliyan 40 kan bukatun kayayyakin more rayuwa a kasashe masu tasowa. A wancan lokacin, Biden ya ce shirin zai fi dacewa da bukatun samar da ababen more rayuwa na kasashe daban-daban fiye da shirin ziri daya da hanya daya da kasar Sin ta gabatar. Amma an kusa soke Shirin, saboda nuna bangaranci a Amurka. Ya zuwa yanzu, adadin kudaden da aka saka a cikin ayyukan da ke da alaka, dalar Amurka miliyan 6 ne kawai, wannan shi ake kira “surutu ba tare da gani a kasa ba".

A halin yanzu, kasashe masu tasowa suna fuskantar babban gibin kudade wajen gina ababen more rayuwa. Hakika abu ne mai kyau, idan har da gaske 'yan siyasar Amurka suna son ba da taimakon kudi. Amma idan har ba sa son baiwa kasashe masu tasowa gudummawa, amma suna son yin wasa da hankali ne, to ko da sabbin sharuddan da suka kirkira don tattara su, ba za su iya yaudarar wasu ba, kuma tun ba a je ko’ina ba,ba za su taba yin nasara ba.(Ibrahim)