logo

HAUSA

An gudanar da dandalin cibiyoyin ilimi na Sin da Afirka na shekarar 2022

2022-06-27 21:08:19 CMG Hausa

A baya bayan nan ne aka gudanar da dandalin masu ruwa da tsaki a fannin raya ilimi na Sin da Afirka na shekarar 2022 ta kafar bidiyo, taron da ya hallara wakilai sama da 1400 daga cibiyoyin ilimi na Sin da na kasashen Afirka, ciki har da malamai, da dalibai daga manyan jami’o’in Sin, Najeriya, da Habasha da sauran su.

Yayin taron na yini 2, masana da kwararru mahalarta, sun yi musayar ra’ayoyi karkashin jigon "Aiki tare don hangen nesa a fannin raya ilimin malanta, da ingiza burin samar da al’umma guda mai makomar bai daya tsakanin Sin da Afirka ".

Cikin jawabin da ya gabatar yayin taron, babban sakataren kwamitin kula da harkokin hukumar UNESCO na kasar Sin Qin Changwei, ya ce bisa ga bukatun kasashen Afirka a fannin raya ilimi, Sin tana raba dabarun ta na ci gaban ilimi da kasashen nahiyar, kana tana tallafawa kasashen na Afirka wajen samar da kwararru a dukkanin sassa, kuma tana ingiza bunkasar harkokin ilimi a nahiyar. (Saminu)