logo

HAUSA

Shugaban Afirka ta Kudu ya nuna alhini game da wasu matasa 22 da suka mutu a wata mashaya a lardin Cape na Gabas

2022-06-27 10:28:54 CMG Hausa

Shugaban Afirka na Kudu Cyril Ramaphosa, jiya Lahadi ya nuna alhini, game da mutuwar wasu matasa 22 a wata mashaya da sanyin safiyar yau a garin East London, dake lardin Cape na Gabas.

Ramaphosa ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, bala'in ya kara girgiza mutane, ganin yadda ya faru a lokacin da ake bikin watan matasa.

'Yan sandan Afirka ta Kudu suna gudanar da bincike kan lamarin, kuma har yanzu ba a san abin da ya haddasa lamarin ba. Haka kuma sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar, ba ta yi karin haske game da musababbin lamarin ba, tana mai cewa, shugaban yana jiran karin bayani.

Ministan kula da harkokin ’yan sanda na kasar Bheki Cele, wanda ya jagoranci tawagar kasar zuwa wurin da lamarin ya faru, ya shaidawa kafofin watsa labarai cewa, akwai su 'yan mata da yara maza a cikin wadanda bala’in ya rutsa da su, ciki har da mai shekara 13. (Ibrahim Yaya)