logo

HAUSA

Ba za mu yi watsi da burinmu na cimma nasara ba(B)

2022-06-27 20:07:22 CMG Hausa

Tunaninta na zama koci, ya fara ne tun Shui Qingxia tana matashiya, a shekarar 1999, kafin ta yi ritaya, ta fara halartar darussan zama koci, ta ce, " Tuni na yanke shawara cewa, ina son zama koci, don haka na fara yin shirye-shirye tun da wuri."

Bayan ta zama koci, ta shafe kusan shekaru 10 a sassan horar da matasa na kasa ko na gida, kuma tana da zurfin fahimtar yadda ake horar da matasa, tsarin bangaren wasan da yanayin al'adu na sana’ar wasan kwallon kafa na mata. Ta bayyana cewa, "Jagorancin kungiyar matasa da kungiyar yara ya sa na ji cewa, neman ci gaban wasan kwallon kafa na mata na kasar Sin ba abu ne mai sauki ba, 'yan mata da ke buga wasan kwallon kafa ba su da yawa, kuma iyaye kalilan ne ke son barin ‘ya’yansu su buga wasan kwallon kafa, wanda hakan ke haifar da wahalar zabar kwararru a fannin."

Matsalolin da Shui Qingxia ta gamu da su a shekaru 10 da suka gabata, sune har yanzu masu horar da matasa suke fuskanta a shekarar 2022.

A shekarar 2010, Shui Qingxia ta koma birnin Shanghai, inda aka nada ta a matsayin mai horar da kungiyar kwallon kafa ta matasa mata ta Shanghai, kuma a shekarar 2011, ta jagoranci kungiyar ta lashe gasar kwallon kafa ta mata 'yan kasa da shekaru 17. Wannan shi ne kofin farko da Shui Qingxia ta lashe a matsayin koci.

A shekarar 2013, ta kai kololuwar aikinta na horarwa a hukumance. A shekarar 2014, ta jagoranci kungiyar lashe gasar kwallon kafa ta mata, kuma a shekarar 2015, ta lashe gasar cin kofin Hukumar Kwallon Kafa ta Sin, da gasar wasan kwallon kafa mata ta Sin wato Women’s Super League, har ma da gasar zakaru ta kasa karo na 13.

A ranar 18 ga watan Nuwamba na shekarar 2021, Hukumar Kwallon Kafa ta kasar Sin ta fitar da sanarwar cewa, Shui Qingxia za ta zama babbar kocin kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasar Sin. A wancan lokacin, kwanaki 63 kawai suka rage kafin a bude gasar cin kofin nahiyar Asiya.

Shui Qingxia ta ce, “Lokacin da na samu labarin nada ni, gaskiya na san zan fuskanci kalubale, na shafe sama da shekaru 30 a harkar kwallon kafa, kuma tunanin kwallon kafa na mata ya dade a cikin zuciyata, kuma a koyaushe ina son zama kocin kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasar Sin."

Har yanzu Shui Qingxia ba ta amince da shan kaye ba, ta ce, “Mutane da yawa na tunanin kafadun mata ba su da karfin daukar kaya, amma ko kungiyar za ta iya cin nasara ko a’a a gasa, wannan ba shi da alaka da jinsin kocin. Na taba rike wannan mukami, kuma na yi nasara, tun da na zabi wannan sana’a, zan zama mai samun nasara, kuma in nuna yadda masu samun nasara suke.”

Har yanzu Shui Qingxia tana iya tuna lokacin da ta fara ganawa da 'yan kungiyar wasan kwallon kafar mata ta kasar, a lokacin kungiyar tana jimamin kayen da ta sha a wasannin Olympics na Tokyo. Shui Qingxia ta ce, “Babban abin da take ji shi ne kungiyar ba ta yi imani da kanta ba. A gani na, wannan ba shi da kyau, dole ne in gyara tunanin 'yan wasan ba tare da bata lokaci ba.”

A hirar ta ta farko bayan zama babbar kocin kungiyar kasar, Shui Qingxia ta gabatar da wata kalma, wato “ 'yan'uwa mata”. Tana fata ‘yan kungiyar za su taimakawa juna kamar yadda 'yan'uwa mata suke yi. Ta ce, “Ba wanda ke farin ciki lokacin da yake cikin koma baya, amma abu mai mahimmanci shi ne yadda za sauya wannan batu. Don haka, tun daga ganawarmu ta farko, na karfafawa kowa da kowa gwiwa, tare da fatan taimakawa dukkan ‘yan kungiyar, ta yadda za su dawo da ruhun juriya da sha'awarsu ta samun nasara.”

Ba da dadewa ba, mun ga wannan canji a fagen gasar cin kofin Asiya, kungiyar kwallon kafar mata ta kasar Sin ta lallasa Taipei ta kasar Sin da ci 4-0, Iran da ci 7-0, sai kuma Vietnam da ci 3-1, kana bayan da suki rashin nasara a baya sau biyu, sun kuma yi kunnen doki sau biyu, kungiyar kwallon kafar mata ta Sin ta kai wasan karshe bayan ta doke Japan a bugun daga kai sai mai tsaron gida. A karshe dai, Tawagar kwallon kafa ta mata ta kasar Sin ta sake lashe kofin gasar Asiya bayan shafe shekaru 16, kuma kasar Sin gaba daya ta shiga farin ciki da aka dade ba a manta ba, sanadiyar kwallon kafa.

Shafin yanar gizon Hukumar Kwallon Kafa Ta Asiya wato AFC a takaice ta taba yin sharhi game da Shui Qingxia: Ta fi kowa sanin yadda za a lashe gasar cin kofin Asiya ta mata.

Mutane na cewa, Shui Qingxia ta dawo da ruhi da halayyar kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasar Sin, kuma ta sauya yanayi da tsarin kungiyar.

A baya jama’a na nuna shakku kan “Ko za ta iya ko ba za ta iya ba”, yanzu mutane suna fatan “Za ta samu nasara yadda ya kamata. Shui Qingxia ba ta damu da abin da jama’a ke fada ba, abubuwan da take tunani har yanzu, abubuwa masu sauki kamar yadda take wasan kwallon kafa a yayin da take matashiya. Ta ce, “ Ni ma ban sani ba ko zan iya ko ba zan iya ba, abu mafi mahimmanci shi ne, a daina wannan tunanin. Ina burin samun nasara, ina fatan ni da kungiyata za mu dan kara kwazo, ina son kara kaimi wannan karon fiye da baya, ta yadda za mu kai kungiyar ga nasara.(Bilkisu Xin)