logo

HAUSA

Habasha na kara nuna sha’awar cinikayyar ridi a kasuwannin Sin

2022-06-26 17:35:40 CMG Hausa

Masu samar da ridi da fitar da shi ketare, sun bayyana matukar sha’awarsu na kara zurfafa huldar cinikayya da kasar Sin, a yayin da ake samun karuwar masaya daga kasar Sin.

Sisay Asmare, shugaban kungiyar masu sarrafa wake da nau’ikan amfanin gona da ake fidda mai da fitar dasu zuwa ketare ta kasar Habasha, (EPOSPEA), ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a baya bayan cewa, kasar Sin ta kasance a matsayin babbar kasuwar da kasar Habasha ke samar mata da ridi a shekaru 10 da suka gabata, yayin da kashi 60 zuwa kashi 70 bisa 100 na ridin Habasha ana fitar da shi ne zuwa kasuwannin kasar Sin.

Alkaluman da kungiyar EPOSPEA ta fitar sun nuna cewa, tsakanin shekarun 2018 zuwa 2021, kasar Sin ta shigo da ridi da adadinsa ya kai ton 282,554 daga kasar Habasha, lamarin da ya sanya ta zama ta farko ta fannin yawan shigowa da ridi daga Habasha.

A cewar Asmare, bikin baje kolin shigi da ficin kayayyakin na kasa da kasa na kasar Sin wato CIIE, ya kasance a matsayin wata muhimmiyar dama ga manyan ‘yan kasuwar dake fitar da kayayyaki ketare a kasar Habasha, inda suka samu karin karbuwa a kasuwannin hada-hadar ridi na kasar Sin, ta hanyar zurfafa hadin gwiwa da takwarorinsu na kasar Sin.

Yace wannan biki ya kasance mai matukar muhimmanci gare su. Sannan  a lokacin da aka shirya bikin, an samu manyan kamfanonin da suka nuna sha’awarsu, kuma sun halarci bikin sau da dama.

Baya ga batun ridi, kasar Habasha tana kuma samun damar kara fadada cinikayyarta da kasar Sin a kasuwannin sayar da koffi, a yayin da kasar ta yankin Asiya ta kasance kasa ta takwas mafi shigo da koffi daga kasar Habasha a cikin shekaru 10 da suka gabata.(Ahmad)