logo

HAUSA

Kasar Sin ta biya dukkan kudin da ya kamata na shirye-shiryen wanzar da zaman lafiya na MDD

2022-06-24 15:53:31 CMG Hausa

 

Ofishin dindindin na kasar Sin a MDD, ya ce kasar Sin ta biya dukkan kudin da ya kamata ta biya, na ayyuka 12 na wanzar da zaman lafiya na MDD, na shekarar kudi ta 2021/2022 a jiya Alhamis.

A cewar ofishin, a matsayinta na mambar dindindin na kwamitin sulhu na MDD, kuma kasa ta biyu mafi bayar da gudunmuwa ga kasafin kudin MDD da na ayyukan wanzar da zaman lafiya, kasar Sin ta kasance mai sauke nauyin dake wuyanta, wanda ke nuna cikakken goyon bayan da take ba MDD da shirye-shiryenta na wanzar da zaman lafiya. (Fa’iza Mustapha)