logo

HAUSA

Jami’in Sin: Taron shugabannin BRICS ya samu kyawawan sakamako

2022-06-24 11:17:53 CMG Hausa

 

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taron shugabannin BRICS karo na 14 da ya gudana a daren jiya, ta kafar bidiyo daga birnin Beijing, fadar mulkin kasar. Yayin taron manema labarai da aka yi bayan taron, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Zhao Xu, ya ce taron ya gudanar cikin nasara, wanda ke da muhimmiyar ma’ana ga makomar kungiyar.

Ma ya furta cewa, a karkashin jagorancin Shugaba Xi, shugabannin kasashen BRICS sun tattauna sosai kan yadda za a raya kyakkyawar huldar abota, a kokarin sa kaimi ga ci gaban duniya. Haka kuma Shugaba Xi ya gabatar da shawarwari guda hudu kan hadin gwiwar kasashen BRICS, wadanda suka bullo da dabarun raya kyakkyawar huldar abota a tsakaninsu, lamarin da ya samu karbuwa daga bangarori daban daban.

Bugu da kari, Ma ya bayyana cewa, an zartas da Sanarwar Beijing ta taron, inda aka bayyana matsayin kasashen BRICS na bai daya kan wasu muhimman batutuwan shiyya-shiyya da na duniya, da nuna sakamakon hadin kansu, kana da tsara shirye-shiryen hadin gwiwarsu a nan gaba.

Ma ya kara da cewa, kungiyar kasashen BRICS wata muhimmiyar alama ce ta ci gaban kasashe masu tasowa. Ya zuwa yanzu dai, kasashen BRICS sun riga sun hada kansu har na tsawon shekaru 16, lamarin da ya zama abin koyi ta fuskar hadin kan kasashe masu saurin ci gaba da masu tasowa. Bana ita ce karo na uku da kasar Sin ta karbi bakuncin taron shugabannin BRICS, inda aka samu dimbin sakamakon hadin gwiwa na a zo a gani a fannonin farfadowar tattalin arzikin duniya, dakilewa da rigakafin yaduwar cutar COVID-19, da raya tattalin arziki bisa fasahar zamani, da neman samun ci gaba mai dorewa, da mu’amalar al’adu. Don haka kasar Sin ta bayar da gudummawarta ga ci gaban hadin kan BRICS. Taron dai ya bude wani sabon babi ga hadin kan kungiyar, wanda ya nuna kyakkyawar makomar tsarin hadin kansu. (Kande Gao)