logo

HAUSA

An gudanr da taron jam’iyyun siyasa na kasashen Sin da Nijeriya

2022-06-24 13:00:52 CMG Hausa

 

Ofishin jakadancin kasar Sin a Nijeriya, da kwamitin kula da jam’iyyun siyasa masu rejista ta kasar (IPAC), sun gudanar da wani taron karawa juna sani mai taken “karfafa hadin gwiwar jam’iyyun siyasa, kara hakuri da juna”, a ranar 22 ga wata.

Mataimakin daraktan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin kolin JKS, Li Mingxiang, ya halarci taron ta kafar bidiyo, wanda ya samu halartar mutane kusan 100, ciki har da Jakadan Sin da ke Nijeriya Cui Jianchun da shugaban kwamitin IPAC kuma shugaban jam’iyyar ADP, Yabaji Sani da Sakataren kwamitin na kasa Yusuf Dantale da shugabanni ko wakilan jam’iyyun siyasa 17 masu rejista na Nijeriya, ciki har da APC da PDP.

A jawabinsa, Li Mingxiang, ya gabatar da manyan nasarori da tarihin JKS cikin shekaru 100 da suka gabata, yana mai cewa, jam’iyyar tana bada muhimmanci ga musaya da hadin gwiwa tsakaninta da takwarorinta na Nijeriya, kuma a shirye take ta kulla abota da su, bisa ka’idojin ‘yanci da daidaito da mutunci da kaucewa tsoma baki cikin harkokin gida da ci gaba da tuntuba da hadin gwiwa kan batutuwan da suka shafe su da kuma inganta hadin gwiwa.

A nasa bangaren, Yabaji Sani, ya taya JKS murnar cika shekaru 101 dake karatowa, yana mai yabawa dimbin nasarorin da al’ummar Sinawa suka samu karkashin jagorancinta. Kana ya jinjinawa rawar ganin da hadin gwiwar Nijeriya da Sin ya taka, wajen inganta tattalin arzikin kasar da walwalar al’ummarta.

Ya ce Nijeriya da Sin manyan kasashe ne masu muhimmin tasiri, kuma ya kamata su hada hannu wajen daukar nauyin inganta zaman lafiya da tsaro da ci gaba da kwanciyar hankali a shiyyoyinsu da ma duniya baki daya.

Bugu da kari, ya ce ya kamata jam’iyyun siyasa a Nijeriya, su yi koyi da JKS wajen shugabantar kasa da kara taka rawa wajen raya demokuradiyya da shugabanci na gari da ci gaban al’umma. Haka kuma, ya ce jam’iyyun Nijeriya za su ci gaba da mara baya ga hadin gwiwar moriyar juna tsakanin Sin da Nijeriya. (Fa’iza Mustapha)