logo

HAUSA

Kasar Sin ce babbar mai bada gudunmawa ga ci gaba mai dorewa a Afrika

2022-06-24 11:11:59 CMG HAUSA

 

An bayyana kasar Sin a matsayin wadda ta fi bada gudnumawa ga ci gaba mai dorewa a Afrika, haka kuma babbar mai taimakawa kasashe masu tasowa.

Mohamed Ibrahim Nasr, daraktan sashen kula da sauyin yanayi da muhalli da ci gaba mai dorewa na ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar ne ya bayyana haka, inda ya bayyana kasar Sin a matsayin daya daga cikin muhimman abokan huldar Afrika a fannin ayyukan ci gaba.

Ya shaidawa Xinhua a gefen taron Zaman Lafiya da Ci Gaba Mai Dorewa na Aswan cewa, bisa taimakon kudi da na kwararru da yadda ta shiga aikin ginin ababen more rayuwa kamar na tashoshin ruwa da gadoji da ayyukan makamashi da sauransu, ana iya ganin kasancewar kasar Sin a kasashen Afrika.

Mohamed Nasr, wanda shi ne babban mai shiga tsakani yayin zama na 27 na taro kan sauyin yanayi na MDD da zai gudana nan gaba a bana, a birnin Sharm El-Sheikh na Masar, ya yabawa kasar Sin bisa rawar da take takawa a fannin taimakawa nahiyar Afrika wajen yaki da matsalolin sauyin yanayi.

Ya ce kasar Sin na taimakawa kasashe masu tasowa akai-akai, musamman na Afrika, wajen gudanar da ayyukan da suka dace da kare muhalli. Yana mai cewa, sauyin yanayi na ci gaba da zama muhimmin abun dake tasiri kan ci gaba mai dorewa a Afrika. (Fa’iza Mustapha)