logo

HAUSA

Mataimakin shugaban Ghana ya bukaci a hada kai a Afrika don tinkarar kalubalolin duniya

2022-06-24 14:05:31 CMG HAUSA

 

Mataimakin shugaban kasar Ghana, Mahamudu Bawumia, ya bukaci kasashen Afrika da su kara zurfafa hadin gwiwar tattalin arziki na shiyyoyi, yayin da ake fama da matsalolin annobar COVID-19 da yakin Ukraine.

Yayin da ya gabatar da jawabin bude babban taron shekara na hukumomin inshorar Afrika (ATI) karo na 22, ya ce, bisa lura da yanayin rage fadin tattalin arzikin kasashen Afrika, akwai matukar bukatar rungumar tsarin bai daya na shiyyoyi, da kuma daukar matakan da suka shafi dukkan nahiyar don tinkarar kalubaloli.

Bawumia ya yi nuni da cewa, taruwar matsalolin mummunan tasirin annobar COVID-19 da yakin Ukraine, babbar barazana ce dake neman durkusar da tattalin arzikin nahiyar, ya bukaci kasashen Afrika da su kirkiro tare da daukar matakan jure yanayin da ake ciki ta hanyar bunkasa cinikayya da kara zuba jari, kuma su yi kokarin kawar da dukkan tsarukan dake haifar da tarnaki ga kamfanoni masu zaman kansu.

Ya kara da cewa, idan Afrika suka yi aiki tare a wannan bangare, za a samu lokaci da kuma damamammakin rage dogaro kan kasuwannin ketare, domin samun bunkasuwar tattalin arzikin nahiyar da kuma samun karin daraja ga albarkatun nahiyar. (Ahmad)