Sin na fatan shigar da tsarin nishadantarwa da motsa jiki cikin makarantun yara
2022-06-23 10:52:28 CMG HAUSA
A wata makarantar midil dake birnin Nanjing na gabashin kasar Sin, yara maza na mata na taka rawar motsa jiki a filin wasan dake harabar makarantar, fuskokin su cike da gumi da murmushi.
Wang Ping ita ce malamar darussan motsa jiki, a makarantar ta midil mai lamba 13, ta kuma bayyana cewa, "Na kwafi wannan salo ne daga wani bidiyon motsa jiki da na ga ya karade shafukan sada zumunta na Douyin, (wanda shi ne shafin TikTok na Sinanci).
Bisa wannan salo, ‘yan makaranta suna tsalle ne yayin daukar darussan motsa jiki, da nufin su rika yin gumi. Hanya ce mai kyau, duba da yadda karin yara Sinawa ke kara nuna sha’awa ga wasannin motsa jiki, kuma ina farin cikin ba da tawa gudummawa a wannan fanni. Ina nazarin karin wasu sabbin dabaru na raya wasanni tsakanin dalibai na, yayin zangon karatun nan”.
Yayin da ake kara fahimtar muhimmancin kula da lafiyar yara, iyayen yara da dama yanzu ba sa kallon motsa jiki a matsayin abu maras muhimmanci, kuma zangon karatu dake tafe, na kunshe da sauye sauye masu ma’ana.
Bisa sabbin ka’idojin da ma’aikatar ilimi ta kasar Sin ta fitar, yara dalibai za su rika shafe shekaru 9 suna karatu na wajibi, wanda zai kunshi karatun firamare da karamar midil, kuma za su rika shiga ajujuwan motsa jiki a kullum nan zuwa shekaru 10 masu zuwa.
Kaza lika, baya ga wasannin da aka saba da su kamar kwallon kafa, da kwallon Kwando da wasannin tsalle tsalle, daliban za su iya zabar shiga darussan gina jikin su domin cimma nasarar cika burin su a wasanni kamar na hawa tsauni, da na zamiyar “skateboard” ko na tsallake igiya.
Wang Zongping, farfesa ne a jami’ar kimiyya da fasaha dake Nanjing. Ya kuma ce ana karfafawa dalibai gwiwar su tsara ajujuwan motsa jiki masu salo daban daban, da sauran abubuwa da za su rika ba su sha’awa, ta yadda hakan zai ba su damar inganta fasahohin su na wasanni, su kuma kara jin dadin gina lafiyar jiki da ta tunanin su.
WASANNI MASU GAMSARWA
A makarantar firamare ta Yuhua dake birnin Nanjing, yin wasan gargajiya na diabolo, ya zamo wasan motsa jiki na yau da kullum tsakanin daliban makarantar su 367. Wasa ne mai ban sha’awa ga kowa. Wasa ne da a cikin sa mutum ke sarrafa jikin sa ta wasa da wasu sanduna biyu da aka kullawa igiya ko zare a karshen su.
A cewar dalibar aji 5 Ma Jiayin "Wannan wasa ya hade wasa da motsa jiki wuri guda, kuma hakan yana ba ni sha’awa. Hakan yana bani dama ta motsa kwakwalwa ta, da karfafa gabobin jiki na, bugu da kari, yana nishadantar da ni"
Shi kuwa shugaban makarantar firamare Shen Zhuzhen, cewa ya yi "burin mu shi ne tabbatar da daliban mu suna cikin koshin lafiya da walwala, don haka makarantar mu ta fara gudanar da ajujuwan wasannin motsa jiki, ciki har da wasa mai salon rawar dabbar dragon mai sigar gargajiya na kasar Sin".
A bara, an kaddamar da manufar ragewa dalibai nauyin yawan ajujuwan da suke halarta, wannan mataki zai ragewa dalibai wahalhalun karatu. Kaza lika manufar ta rage adadin ayyukan gida da dalibai za su rika yi, da yawan jarrabawa da dalibai kan yi yayin da suke karatu, da ma rage dararrusan bayan makaranta da dalibai ke yi a gida. Tun daga nan ne kuma, makarantu da iyalai suka kara maida hankali ga wasanni.
Rawar bamboo, wadda rukunin daliban wata firamare dake lardin Guangxi Zhuang dake kudancin kasar Sin suka nuna ta kafar sada zumunta, ta samu karbuwa da yabo sosai. Tsarin rawa ne da makarantar ta tsara mai kunshe da rawar gargajiya da fasahohin motsa jiki.
Yayin wata rawa da daliban makarantar midil mai lamba daya dake lardin Jiangsu a gabashin kasar Sin suka gudanar, dalibai 2,500 sun rika rawa suna zagayawa da salo tamkar tafiyar maciji. Malamin ajin motsa jiki na makarantar Chen Jianming, ya ce "Muna fatan kara shigar da nishadi cikin motsa jiki, ta yadda dalibai za su kara maida hankalin su kan hakan. Ta wannan dabara, dalibai za su samu damar motsa jikin su a lokaci guda kuma suna karfafa fasahar yin ayyuka tare".
Bisa karsashin da gasar Olympics ta birnin Beijing ta 2022 ta samar ga kasar Sin baki daya, yanzu haka karin yara ‘yan makaranta na tururuwar shiga wasannin kankara da na dusar kankara. Ya zuwa karshen shekarar 2021, sama da makarantu 2,800 a sassan kasar Sin daban daban sun shigar da wasannin hunturu cikin jadawalin darussan su.
MUHIMMANCIN KULA DA LAFIYA
Karancin motsa jiki na da nasaba da taruwar kiba, wadda ke barazana ga lafiyar matasan yanzu. A cewar wani rahoto da cibiyar lura da lafiyar yara ta kasar Sin ta fitar a shekarar bara, adadin yara ‘yan makarantar firamare da na sakandare dake da nauyi fiye da kima, da masu teba ya karu da kaso 8.7 bisa dari tsakanin shekarar 2010 zuwa 2019.
Sakamakon binciken da hukumomin lafiya na kasar Sin suka yi a shekarar 2020, jimillar adadin masu karancin gani tsakanin matasan Sinawa ya kai kaso 52.7 bisa dari, kana adadin masu ciwuka masu nasaba da kwakwalwa, da masu ciwon damuwa tsakanin wannan rukuni tsakanin shekarun 2019 zuwa 2020 ya kai kaso 24.6 bisa dari.
Amma a cewar kocin wasan damben Boxing dan asalin kasar Croatian Goran Martinovic, wanda ke jagorantar wani gidin motsa jiki dake lardin Jiangsu "Motsa jiki na da wasu karin fa’idoji baya ga karfafa gabobi. Ciki har da sanya nishadi, da sa mutum jin farin ciki. A cikin shekarun baya bayan nan, na lura karin yara Sinawa suna rungumar harkokin motsa jiki”.
Kaza lika shi ma wani kundin dokar harkokin wasanni da motsa jiki na kasar Sin, wanda aka yiwa gyaran fuska a baya bayan nan, ya bayyana bukatar cibiyoyin ba da ilimi, da sassan bunkasa wasanni, da makarantu, da iyaye, su rika karfafawa matasa gwiwar shiga wasanni, domin kare kai, da shawo kan matsalolin gani da na kiba fiye da kima.
Game da hakan, Jin Hao, kocin wasan takobi na fencing a makarantar “Royal Grammar” dake birnin Nanjing ya ce "Mun tsara kwasa kwasai gwargwadon shekarun dalibai, domin taimaka musu wajen karfafa lafiyar jikin su, da inganta damar su ta shiga wasannin motsa jiki”.
Wannan makaranta dai na dora muhimmanci sosai ga fannin motsa jiki, inda ta shigar da sama da kwasakwasai 20 na wasanni cikin manhajojin karatu, ciki har da fencing, da kwallon tennis, da wasan tsallake shigaye da dawaki ko “equestrianism” a turance, kuma akwai wasannin da ake yi a rufaffen zaure da girman sa ya kai sama da sakwaya mita 8,000.
Shen Zihao, dalibi ne dan aji 8 a makarantar, wanda kuma ke matukar son wasan jefa faifai na “Frisbee”, ya ce "Yanzu haka ina iya motsa jiki da tsalle sama da a baya, sakamakon horo da nake yi a yau da kullum, kuma a yanzu na kara fahimtar dabarun yin abubuwa tare da abokan wasa. A wasanni da dama, ba za ka iya yin nasara kai kadai ba. Ba wai samun nasara ne kadai ke da muhimmanci ba, haka abun yake a fannin ayyukan karatu da na rayuwa”