logo

HAUSA

CNTAC: Haramcin da Amurka ta sanyawa kayayyakin Xinjiang ya saba dokokin ciniki

2022-06-23 13:44:52 CMG HAUSA

     

Kungiyar kare muradun kamfanonin samar da tufafi na kasar Sin CNTAC, ta ce haramcin da Amurka ta sanyawa dukkan kayayyakin da ake samar a yankin Xinjiang Uygur mai cin gashin kai na kasar Sin, ya sabawa dokokin cinikayya da tattalin arziki na kasa da kasa.

CNTAC ta ce, tana adawa mai tsanani game da matakin Amurka na haramcin da ta sanya, wanda ba kawai yana haifar da mummunar illa ga moriyar kamfanonin saka tufafi na kasar Sin ba ne, har ma zai haifar da illoli ga tsarin dokokin kamfanonin saka tufafi na duniya.

A cewar kungiyar ta CNTAC, audugar Xinjiang, wacce take da matukar daraja da samun karbuwa a duniya, ta kasance a matsayin kashi 20 bisa 100 na jimillar audugar da ake samarwa a duniya, kuma tana da matukar muhimmanci game da tasirin samar da dawwamman ci gaba ga kamfanonin saka tufafi na kasar Sin da ma na duniya baki daya.

Ta kara da cewa, yunkurin Amurkar tamkar nuna kiyayya ne da neman danne hakkokin kamfanonin saka tufafi na kasar Sin, kungiyar ta ce matakin yana matukar haifar da mummunar illa ga tsaro da zaman lafiyar kamfanonin, da ma tsarin hada-hadar cinikayyar kamfanonin saka tufafi na kasa da kasa, kuma yana lahanta moriyar ma’aikatan kamfanonin saka tufafi na kasa da kasa. (Ahmad)