logo

HAUSA

Dokar da Amurka ta sanya mai nasaba da Xinjiang wata alama ce na yunkurin dakile tsarin masana'antun kasa da kasa

2022-06-23 19:08:00 CMG Hausa

A ranar 21 ga watan Yuni ne, Amurka ta ke tunanin cewa, wai dukkan kayayyakin da ake samarwa a yankin Xinjiang na kasar Sin, suna da alaka da abin da ta kira wai “aikin tilas” tare da hana shigo da duk wani nau’in kayayyakin da suka shafi Xinjiang cikin kasar ta Amurka.

Amurka ta kirkiri abin da ake kira "aikin tilas", inda ta kitsa karya a wani yunkuri na mayar da dukkan kayayyakin da ke da alaka da Xinjiang saniyar ware, kuma hakan tamkar kebe kanta ne Amurkar ta yi daga kasuwannin duniya. (Ibrahim)