logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Nuna Damuwa Kan Yadda ‘Yan Sandan Amurka Suka Kashe Mutane Ba Bisa Doka Ba

2022-06-23 11:46:29 CMG HAUSA

Wakilin kasar Sin ya nuna damuwa kan yadda ‘yan sandan kasar Amurka suka kashe mutane ba bisa doka ba, yayin da yake tattaunawa da mai sa ido kan batun kashe mutane ba bisa doka ba, a wajen taron kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD karo na 50 jiya Laraba.

Wakilin kasar Sin ya nuna cewa, an sha jin labaru masu tarin yawa dangane da yadda ‘yan sandan Amurka suka ci zarafin wasu yayin da suke aiwatar da doka. An ruwaito cewa, a cikin shekara guda bayan mutuwar George Floyd, wanda ya mutu sakamakon cin zarafi yayin da ‘yan sandan Amurka suke aiwatar da doka, masu aiwatar da doka na Amurka sun kashe darurruwan ‘yan kananan kabilu a kasar. Haka kuma sojojin Amurka sun kashe fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba yayin da suka gudanar da ayyukan soja a ketare, amma ba a gurfanar dasu a gaban kotu ba.

Wakilin kasar Sin ya kalubalanci kwamitin kare hakkin dan Adam da kuma mai sa ido kan batun kashe mutane ba bisa doka ba, da su rika mai da hankali kan yadda ‘yan sandan Amurka suka ci zarafin wasu yayin da suke aiwatar da doka, da kuma yadda sojojin Amurka suka kashe fararen hular da ba su ji ba ba su gani ba ‘yan kasashen waje, a kokarin kara azama kan gudanar da cikakken bincike kan batutuwa masu ruwa da tsaki cikin adalci da kuma gurfana da masu aikata laifin. (Tasallah Yuan)