logo

HAUSA

Amsar "Tambaya kan halin da ake ciki"

2022-06-23 20:38:38 CMG Hausa

"Ina duniya ta dosa ne?" A yayin bikin bude dandalin kasuwanci na BRICS da aka gudanar a yammacin jiya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wani muhimmin jawabi ta kafar bidiyo wanda ya tabo "tambaya game da halin ake ciki".

Shugaba Xi ya bayyana cewa, “Dole ne mu hada kai tare, don wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya baki daya", "Dole ne mu taimaki juna tare da inganta ci gaba mai dorewa a duniya baki daya", "Dole ne mu taimaki juna don cimma hadin gwiwar samun nasara tare", "Dole ne mu yi hakuri ga juna don kara bude wa juna kofa”, shawarwari 4 da Xi Jinping ya gabatar, sun nuna muradin bai daya na al'ummomin kasashen duniya, kuma ya zama cikakkiyar amsa game da "tambaya kan halin da ake ciki ". (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)