logo

HAUSA

Girgizar kasa ta yi sanadin mutuwar akalla mutane 280 tare da jikkata wasu 595 a Afghanistan

2022-06-23 10:49:42 CMG Hausa

Akalla mutane 280 sun mutu, wasu 595 kuma sun jikkata, sanadiyyar wata girgizar kasa da ta aukawa lardin Paktika ta Afghanistan da safiyar ranar Laraba.

Rahoton kamfanin dillancin labarai na Bakhtar na kasar, ya ce tuni dai jirage masu saukar ungulu da tawagogin ceto suka isa wurin da iftila’in ya auku.

A cewar hukumar nazarin kasa ta Amurka, girgizar kasar mai karfin maki 6.1, ta girgiza kudu maso yammacin yankin Khost.

Majiyoyi a cikin kasar, sun ce iftila’in ya lalata gomman gidaje a yankin tare da haifar da zaftarewar kasa a Paktika. (Fa’iza Mustapha)