logo

HAUSA

Akwai Makoma Mai Haske Game Da Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

2022-06-23 18:38:22 CMG Hausa

A baya bayan nan, hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana raguwar adadin masu harbuwa da cutar COVID-19 a nahiyar Afirka da kaso mai yawa, tun daga tsakiyar watan Afirilun da ya gabata, raguwar da a cewar hukumar ita ce mafi tsawo da aka samu a nahiyar tun bullar wannan annoba kawo yanzu.

Ko shakka babu wannan labari ne mai faranta rai ga duniya baki daya. To sai dai kuma, wani jan aiki dake gaban kasashen nahiyar ta Afirka a yanzu shi ne lalubo hanyoyin shawo kan mummunan tasirin da wannan annoba ta haifar musamman ta fuskar tattalin arzikin Afirka. Hakan ne ma ya sa masharhanta da dama ke ganin ya zama wajibi kasashen Afirka su karfafa hadin gwiwarsu da kasar Sin, karkashin muhimman manufofin hadin kai da sassan biyu suka jima da amincewa da su, wadanda suka hada da manufofin da aka tsara karkashin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, da ayyukan samar da moriya dake kunshe cikin shawarar nan ta “ziri daya da hanya daya” da sauran su.

A halin da ake ciki, kasar Sin ce babbar abokiyar huldar nahiyar Afirka ta fuskar kasuwanci cikin sama da shekaru 10, kuma kasar da kamfanoninta ke kara zuba jari mai yawan gaske a nahiyar, wanda adadinsa ya karu a watanni 7 na farkon shekarar 2021 zuwa dalar Amurka biliyan 2.07.

A bangaren nahiyar Afirka, masana na cewa, nahiya ce dake da tarin albarkatun kasa, da ma’adanai masu daraja, da man fetur da iskar gas, da damar samar da makamashi daga hasken rana, da fadin kasar noma mai yalwa, da tarin al’umma dake cikin shekarun kwadago. Sai dai kuma kalubalen rashin masana’antu, da kamfar makamashi, ya zamowa nahiyar “kadangaren bakin tulu”, ta yadda kasashen nahiyar ba sa samun damar cin gajiyar da ta dace daga albarkatunta. Hakan ya sa kasashen Afirka da dama kasancewa cikin jerin kasashe mafiya fama da talauci a duniya.

Duk da wadannan tarin kalubale, akwai makoma mai haske ga kasashen na Afirka, muddin sun ci gaba da nacewa aiwatar da kudurorin dake kunshe cikin ajandojin wanzar da ci gaban su, tare da babbar manufar nan ta raya hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ta nan da shekarar 2035, ko “China-Africa Cooperation Vision 2035” a Turance, da ma shirin dandalin bunkasa hadin gwiwar Sin da Afirka na Dakar, mai kunshe da tsarin ayyuka da za a aiwatar tsakanin shekarar nan ta 2022 zuwa 2024. Dukkanin wadannan kudurori ne da ke kunshe cikin babbar manufar nan ta shawarar “ziri daya da hanya daya” da kasar Sin ta gabatarwa duniya, wadda ko shakka babu, ci gaba da aiwatar da ita zai haifarwa kasashen na Afirka tarin alfanu nan da shekaru masu zuwa. (Saminu Hassan)