logo

HAUSA

An kammala taron tattauna zaman lafiya na Sin da kusurwar Afrika karo na farko

2022-06-23 14:22:14 CMG HAUSA

 

An kammala taron zaman lafiya da samar da ingantaccen shugabanci da ci gaba na Sin da kusurwar Afrika karo na farko a ranar Talata a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, inda aka yi kiran hadin gwiwa don cimma muradun bai daya na shiyyoyin.

Mahalarta taron na kwanaki biyu da aka kammala, sun tattauna tare da fidda sanarwar hadin gwiwa kan wasu muhimman batutuwa goma sha biyu.

Sanarwar hadin gwiwar ta bayyana cewa, shiyyar kusurwar Afrika wato HOA, wani muhallin zama ne ga al’ummar dake shiyyar, kana ana bukatar samun tabbatar da zaman lafiyar shiyyar, da kwanciyar hankali, da ci gaba, sannan neman makoma mai kyau shi ne muhimmin ginshiki na moriyar dukkan kasashen duniya kuma shi ne babban muradi na dukkan al’ummar shiyyar.

Bugu da kari, sun bayyana aniyarsu na samun kyakkyawan shugabancin siyasa, da daukar kwararan matakan gina cigaba, da kawar da rashin fahimta da rashin jituwa a tsakanin kasashen shiyyar, da kokarin neman zaman lafiya ta hanyar tattaunawar sulhu don cimma nasarar saukaka yanayin tsaro a kasashen shiyyar.

Kasashen shiyyar sun kara yabawa kasar Sin sakamakon bullo da wannan taro, da nufin kyautata makomar zaman lafiyar kusurwar Afrika, da samar da shugabanci na gari da ci gaba, da yadda kasar ke kokarin tsayawa tsayin daka wajen aiwatar da muradun ci gaban kasa da kasa, da shawarwarin tabbatar da tsaron kasa da kasa.

A cewar sanarwar hadin gwiwa, kasar Sin ta tabbatar da aniyarta na yin amfani da shawarar ziri daya da hanya daya da aiwatar da sakamakon da aka samu a taron kolin FOCAC da manufofin cigaban kasashen shiyyar. (Ahmad)