logo

HAUSA

Hukumar kare muhalli ta duniya ta amince da dala miliyan 18 don ayyukan kare halittu da albarkatun ruwa

2022-06-23 11:14:34 CMG HAUSA

 


Shirin hukumar kare muhallin ta duniya (GEF), ya amince da gudanarwa da wasu ayyuka uku karkashin jagorancin hukumar kula da abinci da ayyukan gona ta duniya (FAO) a kasashe biyar, inda za a kashe jimillar kudi dala miliyan 18 don gudanar da ayyukan, kamar yadda hukumar ta FAO ta bayyana cikin wata sanarwa.

Za a gudanar da sabbin ayyukan ne a kasashen Najeriya da Venezuela da kuma wasu shiyyoyin kasashen Malawi, da Mozambique da Uganda. ana fatan ayyukan za su inganta kare muhallin yankuna a kasashen, da kare nau’ikan halittun dake dazuka, da kuma gina tsarin adanawa da kula da albarkatun ruwa, kamar yadda sanarwar da FAO ta fitar wadda kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu a Legas, cibiyar kasuwancin Najeriya.

Maria Helena Semedo, mataimakiyar babban daraktan hukumar FAO ta bayyana cewa, tabbatar da ingantaccen tsarin kula da gonaki da muhallin halittun ruwa, sun kasance a matsayin wasu manyan ginshikan samar da dawwamamman cigaban shirin bunkasa samar da abinci da aikin gona.

Semedo ta kara da cewa, amincewar da aka yi don gudanar da wadannan ayyuka uku za su kara karfafa gwiwar tallafawa kasashen duniya wajen dora su kan turbar samar da ci gaba mai dorewa ba tare da an bar wani bangare a baya ba.

A cewar sanarwar, aikin da za a gudanar a Najeriya, zai inganta kare gandun daji, da amfani mai dorewa, da farfado da dazuka, da yanayin tsara gonaki, domin bada gagarumar gudunmawa ga shirin kare halittun kasa da kasa, da kuma karfafa samun dawwamman cigaba na yanayin zaman rayuwar al’ummun kasashen. (Ahmad Fagam)