logo

HAUSA

Dokar Hana Aikin Tilas Ko Dokar Neman Durkusar Da Tattalin Arzikin Sin?

2022-06-22 18:33:58 CMG Hausa

Amurka ta fara amfani da dokar da ta zartar dake ikirarin hana aikin tilas a jihar Xinjiang ta kasar Sin a jiya. Dokar na nufin kin karbar kayayyakin da aka samar a jihar, har sai an gabatar da shaidun dake tabbatar da cewa, ba ta hanyar aikin tilas aka samar da su ba.

Rahotanni sun nuna cewa, Xinjiang ce ke samar da kaso 20 na audugar da ake amfani da ita a duniya. Kuma a lokacin girbin auduga, ba al’ummar jihar kadai ba, har wasu daga sauran sassan kasar Sin na zuwa Xinjiang domin gudanar da aiki don samun karin kudin shiga. Shin idan har da gaske aikin tilas suke yi, me ya sa wasu za su niki gari su tafi inda ake aikin tilas? Wannan ikirari na Amurka na tattare da ayoyin tambaya.

Sanin kowa ne cewa, rashin aikin yi, shi ne tushen rikici a yankuna daban daban. A ganina, ban da saurin ci gaban tattalin arzikin Sin mai juriya da ya tsonewa Amurka ido, akwai ma zaman lafiya da kasar ke morewa da kuma ammana da gwamnati da al’ummarta suka yi, wanda ya yi hannun riga da yanayin Amurka.

Kullum Amurka da kawayenta na yayata batun kare hakkin dan Adam a jihar Xinjiang, amma abubuwan da take yi ba sa dacewa da furucinta. Wannan doka a ganina, wani yunkuri ne na dankwafe ci gaban tattalin arzikin Sin da ma musgunawa al’ummar Xinjiang da take ikirarin karewa. Tun da noman auduga jigo ne a jihar Xinjiang, me zai faru idan aka daina sayen audugar a duniya? Wannan ba shi ne keta hakkin bil adama ba? Wato toshe musu hanyar samun kudin shiga, da zai shafi walwalarsu da yanayin zaman takewa.

Kamata ya yi Amurka ta zartar da dokokin da za su amfani al’ummarta kamar na hana mallakar bindiga da yaki da annobar COVId-19 da tunkarar matsalar tashin farashin kayayyaki, ba zartar da dokokin kan kayayyakin Sin ba. Wannan mataki na Amurka, ba kamfanonin Xinjiang za su shafa kadai ba, har da kamfanonin Amurkar. Idan Amurka ba ta duba halin da za ta jefa ma’aikata da kamfanonin Sin ba, ai ya kamata ta duba na al’ummarta idan har ta damu da su.

An riga an shaida cewa, tubalin karfin tattalin arzikin kasar Sin ne samun gagarumar gudunmawa daga kasuwar cikin gida saboda yawan al’ummarta. Kana ba Amurka ce kadai ke cinikayya da Sin ba, don haka, matakin ita da al’ummarta zai fi yi wa tasiri ba kasar Sin. (Faeza Mustapha)