logo

HAUSA

Rahotanni game da kalaman Tedros cewa, COVID-19 na iya bulla daga dakin gwaje-gwajen Wuhan ba gaskiya ba ne

2022-06-22 19:35:26 CMG Hausa

Wasu rahotanni na cewa, a baya-bayan nan babban darektan hukumar lafiya ta duniya (WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana a asirce cewa, "Mai iyuwa asalin COVID-19 na iya bulla daga dakin gwaje-gwajen Wuhan." Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana Larabar nan cewa, sakatariyar hukumar ta WHO ta yiwa bangaren kasar Sin karin haske, yana mai jaddada cewa, babban darektan hukumar bai furta irin wadannan kalamai a bainar jama'a ko a boye ba, kuma bayanan da aka bayar gaba daya ba gaskiya ba ne. Babban darektan da kansa bai amince da abubuwan da suka shafi wannan batu a cikin rahoton ba. (Ibrahim)