An Bude Sabon Babi A Yankin Hong Kong
2022-06-22 18:33:08 CMG Hausa
Sanin kowa ne cewa, kiyaye tsaron kasa, batu ne da ya shafi muhimman muradun kowace kasa a duniya. Kuma tun bayan da yankin musamman na Hong Kong ya dawo karkashin ikon kasar Sin, bisa ka'ida ta 23 cikin babbar dokar yankin, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta dankawa yankin izinin kafa dokarsa ta fannin kiyaye tsaron kasa.
Sai dai kafin kammala aikin kafa dokar, yankin ya fuskanci wasu ’yan hatsaniya, na rashin doka a bangaren tsaron kasa, wanda masana ke cewa, ba ya rasa nasaba da tsoma baki cikin harkokin yankin daga ketare.
Duk mai bibiyar al’amuran yau da kullum, ya ga yadda a ’yan shekarun baya-baya, wasu bata-gari suka yi yunkurin balle Hong Kong daga kasar Sin, da cin zarafi gami da lalata tambari da tutar kasa, da zuga al'umma don su mamaye ofishin gwamnatin tsakiya dake Hong Kong, da kai harin kan mai uwa da wabi, da cin zarafin 'yan sanda wadanda a kullum suke sadaukar da rayukansu don tabbatar da tsaron al’umma, al'amuran da suka kasance ayyukan ta'addanci, da haifar da babbar barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a Hong Kong gami da cikakken iko na kasa. Kuma duk wata kasa da ta san abin da take yi, ba za ta amince da irin wannan danyen aiki ba.
Kamar kowace kasa mai cikakken ’yanci, ita ma kasar Sin tana da ’yancin kafa dokokin da za su dace da yanayi da ma tsarin tafiyar da cikakkun yankunanta. Kuma tun lokacin da aka kafa, tare da fara aiwatar da dokar tsaron kasa mai nasaba da yankin Hong Kong, wadda wata muhimmiyar dama ce ta yanke hukunci ga baragurbin dake neman ta da rikici a yankin, lamarin da ya tabbatar da ci gaba mai dorewa a yankin, da ma tafiyar da tsarin nan na kasa daya amma tsarin mulki iri biyu yadda ya kamata.
Jagororin yankin dai sun sha nanata cewa, masu bin doka suna maraba da dokar tsaron da aka kafa, matakin da ya kara janyo masu sha’awar zuba da neman halaliya tare da kara dawo da martabar yankin a idon duniya.
Yanzu dai yankin Hong Kong ya zabi shugabanni masu kishin kasa, wadanda za su fara aikin jan ragamar harkokin yankin daga ranar 1 ga watan Yulin wannan shekara. Matakin da masu sharhi ke cewa, ya bude wani sabon babi a yankin, tun bayan da aka kafa sabbin dokokin tsaron kasa da na zabe masu alaka da yankin.
Burin kowace kasa mai ’yanci dake da kishin muhimman muradun al’ummomin ta, shi ne kare rayuka da dukiyoyin jama’a maimakon zangar-zangar da za ta kai ga koma bayan kasa da al’ummarta a dukkan fannoni. Kuma kowa da irin kiwon da ya karbe shi.
Duk wata kasa mai cikakken ’yanci, wajibi ne tana da dokar tsaron kasarta. Kuma duk wanda ya karya doka, tilas ne doka za ta taka shi. Da ma “Icce aka ce, tun yana danye ake lankwasa shi”. (Ibrahim Yaya)