Matakan da kasar Sin ta dauka wajen aiwatar da shawarar bunkasa duniya
2022-06-22 09:03:54 CMG Hausa
A wannan mako ne, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya halarci taron gabatar da rahoto game da ci gaban duniya, bikin da ya gudana ta kafar bidiyo.
A yayin jawabin nasa Wang Yi ya jaddada cewa, hangen nesan Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kan amfana wa daukacin bil Adama, inda ya gabatar da shawarar bunkasa duniya a wajen taron majalisar dinkin duniya, da gaggauta aiwatar da ajandar majalisar ta neman samun dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030, a kokarin sa kaimi ga ci gaban duniya yadda ya kamata.
Ban da wannan kuma, Wang Yi ya bayyana cewa, cikin rahoton ci gaban duniyar, kasar Sin ta baiwa ajandar MDD shawarwari a fannoni 8, bisa kyawawan sakamako da fasahohin da Sin da kasashen duniya suka samu.
Wannan wani muhimmin mataki ne da kasar Sin ta dauka wajen aiwatar da shawarar bunkasa duniya, wanda zai taimakawa daukacin kasasehn duniya wajen kara samun ci gaba, da samar da dabaru ga sha’anin ci gaban duniya.
Har kullum kasar Sin na bayyana kudirinta na yin aiki kokari tare da bangarori daban daban wajen aiwatar da shawarar bunkasa duniya, da gaggauta aiwatar da ajandar MDD, a kokarin raya kyakkyawar makomar ci gaban duniya ta bai daya.
Jami’in na kasar Sin ya kuma gabatar da cewa, duniya na bukatar zaman lafiya da warware dukkan matsaloli ta hanyar tattaunawa da taimakawa kasashe masu tasowa da fasahohi da dabaru, don inganta kwarewarsu ta samun bunkasuwa, da mutuntawa da martaba juna, ta yadda za a gudu tare a tsira tare. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)