logo

HAUSA

Sin Ta Kira Taron Tattauna Mumunan Tasirin Da Manufar Mulkin Mallaka Ya Haifar Ga Hakkin Bil Adama

2022-06-22 12:29:25 CMG HAUSA

DAGA CMG HAUSA

 

Yayin taro karo na 50 na majalisar kula da kare hakkin Bil Adam ta MDD, tawagar dindindin ta kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva, ta kira taron tattauna mumunan tasirin da manufar mulkin mallaka ta haifar ga hakkin bil Adam ta kafar bidiyo.

Chen Xu, Wakilin dindindin na tawagar kasar Sin dake ofishin da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake Switzerland, ya bayyana cewa, kamata ya yi bangarori daban-daban su dukufa kan kawar da mumunan tasirin da manufar mulkin mallaka ya haifar musamman ma a fannin hakkin bil Adam, ta yadda za a tabbatar da adalci a duniya da ingiza bunkasar aikin kare hakkin bil Adam.

Farfesa a kwalejin shari’a ta jami’ar Wuhan ta kasar Sin, Zhang Wanhong da masana daga Afrika ta kudu da Indiya da Zimbabwe, sun bayyana ra’ayoyinsu a fanonnin da suka yi nazari game da mumunan tasirin tsarin mulkin mallaka, inda suka bayyana cewa, Amurka da Birtaniya da sauran kasashen Turai, sun jefa mutanen da suka yiwa mulkin mallaka cikin masifa, saboda irin kisan kare dangin da suka yi musu. Amma, wadannan kasashe ba su dubi laifufukan da suka aikata ba, inda suke ci gaba da tsoma baki kan harkokin cikin gidan sauran kasashe bisa fakewa da batun hakkin bil Adam. Kuma suna amfani da karfinsu a fannin tattalin arziki da tsare-tsaren da suka kafa, wajen ware kasashe masu tasowa daga tsarin tattalin arzikin duniya ta hanyar fakewa da batun hakkin bil Adam da kwadago da ma’aunin muhalli da sauransu, ta yadda za su ci gaba da