logo

HAUSA

Sin da Equatorial Guinea sun rattaba hannu kan musayar bayanai don taimakawa aikin gona a Equatorial Guinea

2022-06-22 19:22:18 CMG Hausa

A ranar 20 ga wata, a ma'aikatar harkokin waje da hadin gwiwar kasar Equatorial Guinea, jakadar kasar Sin dake kasar Equatorial Guinea Qi Mei da ministan harkokin wajen Equatorial Guinea Simeon Oyono Angue, suka rattaba hannu kan musayar bayanai a madadin gwamnatocin kasashen biyu, don taimakawa fasahar aikin gona a kasar

Uwar gida Qi Mei ta bayyana cewa, kasar Sin tana fatan tallafawa kasar Equatorial Guinea, don raya aikin gona na zamani bisa karfin kanta, da inganta karfinta na tabbatar da samar da abinci.

A nasa jawabin minista Simeon Oyono Angue ya bayyana cewa, taimakon da kasar Sin ta samarwa kasarsa ya haifar da sakamako mai gamsarwa, wanda ya ba da muhimmiyar gudummawa ga kokarin da kasar Equatorial Guinea ke yi na kara samar da amfanin gona, da wadatar abinci. (Ibrahim)