logo

HAUSA

An kaddamar da taron Aswan da ya mayar da hankali kan matsalolin Afrika

2022-06-22 12:09:02 CMG Hausa

 

An kaddamar da taron Aswan domin ci gaba da zaman lafiya mai dorewa karo na 3, inda yake mayar da hankali kan matsalolin da Afrika ke fuskanta, musamman karancin abinci da sauyin yanayi da yaki da ta’addanci.

Cikin sakonsa na bidiyo ga taron da aka kaddamar jiya a birnin Cairo na kasar Masar, sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya ce, al’ummar Afrika na fuskantar tarin matsalolin da ba a taba gani ba.

Ya kara da cewa, yayin da take fama da tasiri mai tsanani na rikicin Ukraine da sauyin yanayi da annobar COVID-19, nahiyar na bukatar karin hanyoyin samun kudi da na saukaka bashi, ta yadda za ta zuba jari a fannin samar da ayyukan yi da rage talauci da kare al’umma da wadatar abinci da raya muhalli.

Da yake jawabi, shugaban Masar, Abdel Fattah al Sisi, ya bayyana matsalar abinci da nahiyar ke fuskanta da tasirinta ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’ummomi, inda ya bukaci kasashen nahiyar su hada gwiwa da sauran kasashen duniya da abokan hulda, domin daukar matakai masu inganci cikin gaggawa.

A nasa bangare, shugaban hukumar AU, Moussa Faki Mahamat, ya shaidawa taron cewa, AU ta tsara wata dabara ta kara yankunan dazuka da rage fitar da sinadaran carbon tare da taimakawa kasashe marasa karfi kara zuba jari wajen samun ci gaba mai dorewa.

Taken taron na yini biyu da aka yi a zahiri da kuma kafar intanet shi ne, “Afrika a Zamanin Tsallake Barazana da Matsalolin Yanayi: Hanyoyin Samun Zaman Lafiya da Juriya da Nahiya Mai Dorewa. (Fa’iza Mustapha)