logo

HAUSA

Shugaban Nijeriya ya bada umarnin gaggauta ceto fasinjojin jirgin kasa da aka sace

2022-06-22 10:40:58 CMG Hausa

 

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya umarci hukumomin tsaro, da su yi amfani da matakan karfi da wadanda ba na karfi ba, wajen ceto mutanen da aka sace bayan harin da aka kai wa jirgin kasa a arewa maso yammacin kasar, kimanin yau watanni 3 da suka gabata.

Sanarwar da kakakin shugaban Garba Shehu ya fitar jiya, ta ce shugaban ya bayar da umarnin ne yayin da gwamnatin ke ci gaba da nazarin batun fasinjojin jirgin kasa da aka sace, domin yi wa tufkar hanci.

Ya ce bisa sahalewar shugaban kasar, gwamnati za ta ci gaba da aiwatar da matakan biyu domin tabbatar da sakin fasinjojin lami lafiya. Yana mai cewa, har yanzu akwai mutane 51 ko fiye da ake rike da su.

Garba Shehu ya kara da cewa, an ba hukumomin tsaro da na tattara bayanan sirri, tabbacin matse kaimi ga ayyukan da za su kai ga ceto dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su, tare da dawo da zaman lafiya a dukkan sassan kasar. (Fa’iza Mustapha)